Dollar

41,2910

0.2 %

Euro

48,4340

0.61 %

Gram Gold

4.758,6800

1.43 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kwanan baya ne Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya halarci baje-kolin kayayyakin yaƙi da ƙere-ƙere na duniya a Istanbul inda Turkiyya ta amince ta sayar da ƙarin jirage mara matuƙa da horas da sojojin Nijeriya kan dabarun yaƙi na zamani.

Tinubu ya amince a sayi ƙarin jirage mara matuƙa don yaƙi da ‘yan bindiga a Arewacin Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce amince ma’aikatar tsaron ƙasar ta sayi ƙarin jirage mara matuƙa domin yaƙi da ‘yan bindiga a Jihar Katsina da sauran sassan ƙasar.

Wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata da maraice ta ce shugaban na Nijeriya ya kuma bayyana cewa za a ƙara yawan dakaru a Jihar Katsina domin hana kai hare-hare kan ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba.

Shugaban ya bayyana wannan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar manyan ‘yan jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Dikko Umaru Radda.

Sanarwar ta ambato Shugaba Tinubu yana cewa: "Yau na ba da umarni ga dukkan jami’an tsaro su ƙarfafa [ayyukansu] su kuma sake nazari kan dabarun yaƙi. Mun amince a sayi ƙarin jirage mara matuƙa.”

"Ƙalubalen da muke fuskanta abubuwa ne da za mu iya cin galaba a kansu. Da gaske muna da iyakoki da babu tsaro. Mun gaji da wannan rauni, ya kamata a ce an magance wannan matsala kafin yanzu. Ƙalubale ne da ya zama dole mu magance shi, kuma muna tunkararsa,” in ji Tinubu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#