Sport
Dollar
41,2910
0.2 %Euro
48,4340
0.61 %Gram Gold
4.758,6800
1.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Fiye da mutum 100 ne a cikin kwale-kwalen lokacin da ya daki wani kututture da ke ƙarƙashin ruwa sannan ya kife a Jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.
Aƙalla mutum 60 sun mutu bayan wani kwale-kwale ɗauke da fiye da mutum 100 ya kife a Jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya, in ji jami’ai.
Kwale-kwalen ya bar Tungan Sule a gundumar Malale da safiyar ranar Talata inda ya nufi garin Dugga domin kai gaisuwar ta’aziyya, a lokacin da ya daki wani kututture da ke ƙarƙashin ruwa kusa da garin Gausawa da ke ƙaramar hukumar Borgu.
"Adadin waɗanda hatsarin ya kashe ya kai 60," kamar yadda Abdullahi Baba Ara, shugaban ƙaramar hukumar Borgu, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters ranar Laraba.
"An samo mutum 10 cikin mawuyacin hali, kuma kawo yanzu ana neman wasu da dama," in ji shi.
Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na safiya kuma ƙarfe 10:00 a agogon GMT.
Sa’adu Inuwa Muhammad, Hakimin Garin Shagumi, ya ce ya isa wurin jim kaɗan bayan aukuwar lamarin.
"Kwale-kwalen ya ɗauki fiye da mutum 100. Mun ciro gawarwaki 31 daga kogin. An kuma samu an ciro kwale-kwalen," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa mata da yara ne suka fi yawa a cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
‘Jirgi mai lodi da yawa’
Comments
No comments Yet
Comment