Sport
Dakarun sojin sun daƙile yunƙurin harin na ‘yan ta’addan da ƙarfin makamai da dabarun yaƙinsu, in ji rundunar ta Operation Hadin Kai.
Sojojin rundunar Operation Hadin kai sun kashe mayaƙan Boko Haram 16 a jihar Borno a ranar Litinin.
Wata sanarwar da kakakin rundunar ta Operation hadin kai, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar, ta ce nasarar kashe ‘yan ta’addan ta biyo bayan harin da mayaƙan suka nemi kaiwa kan sojoji ne ranar 5 ga watan Fabrairu a sansanin sojin da ke Auno.
Dakarun sojin sun daƙile yunƙurin harin na ‘yan ta’addan da ƙarfin makamai da dabarun yaƙinsu, in ji rundunar ta Operation Hadin Kai.
Dakarun da suke aiki tare da ‘yan-sa-kai sun ƙaddamar da harin ramuwa kan ‘yan ta’addan ranar 9 ga watan Fabrairu ta hanyar Komala da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno, in ji sanarwar.
“Dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan da ke ja da baya kusa da Gidan Kaji inda suka kashe 16 , tare da tilasta wa wasu da dama tserewa bayan ji musu rauni,” in ji Laftanal Kanal Uba.
Kazalika dakarun sun ƙwace kekuna fiye da 20 da kayayyaki da dama da makamai da sauran muhimman abubuwa daga ‘yan ta’addan.
“A wani lamari da ya sake raunata harkar samar da kayayyaki ga ‘yan ta’addan, dakaru suna kama wasu da ake zargi da safarar kayayyaki wa ISWAP yayin da suke tafiya da magunguna da yawa domin kai wa ‘yan ta’adda a yankin Bukarti a ranar,” in ji sanarwar.
Har ila yau, dakaru sun daƙile ƙoƙarin garkuwa da mutane a kan hanyar Buratai zuwa Kamuye.
Sanarwa ta ce dakarun sun kuɓutar da Malam Idris Adamu da Malam Muhammadu Safiyanu, daga hannun ‘yan ta’adda tare da haɗa su da iyalansu a Buratai.
Comments
No comments Yet
Comment