Dollar

43,2984

0.06 %

Euro

50,7875

0.05 %

Gram Gold

6.765,7300

2.23 %

Quarter Gold

11.271,7300

3.07 %

Silver

131,1000

-0.02 %

Rundunar Hadin Kai ta Sojin Nijeriya ta gano wani wuri da mayakan kungiyar Boko Haram suke boye magunguna da man fetur da sauran kayayyakin da suke amfani da su, bayan da rundunar ta kai samame wurare da dama a yankin Timbuktu Triangle da ke Borno.

Sojoji sun gano wurin da ’yan Boko Haram suke ɓoye man fetur a ƙarƙashin kasa a Borno

Rundunar Hadin Kai ta Sojin Nijeriya ta gano wani wuri da mayakan kungiyar Boko Haram suke boye magunguna da man fetur da sauran kayayyakin da suke amfani da su, bayan da rundunar ta kai samame wurare da dama a yankin Timbuktu Triangle da ke Borno.

Hakan ya biyo bayan jerin hare-haren da aka kai a ranar Lahadi a Chilaria, Garin Faruk and Abirma inda dakarun suka kawar da hare-hare da dama da ’yan ta’adda suka aika musu ta amfani da jirgi mara matuki.

Jami’in Yada Labarai na Reshen Hadin Gwiwa a Shiyyar Arewa maso Yamma ta Rundunar Hadin Kai Laftanal Kanal Uba Sani ne bayyana haka a wata sanarwa da ya fita ranar Litinin.

Kamar yadda jami’in hulda da jama’ar ya bayyana ya ce an kai farmakin ne karkashin Rundunar Desert Sanity wanda kuma ya yi sanadin lalata sansanonin ’yan ta’adda da dama. Kazalika hare-haren sun jawo wa kungiyoyin Boko Haram da ISWAP asara mai yawa.

Sannan ya kara da cewa a ranar Lahadi 18 ga watan Janairun shekarar 2026 dakarun Nijeriya suka kai wasu hare-hare bayan samun wasu bayanan sirri inda suka kai hare-hare a maboyar ’yan ta’addan a Chilaria da Garin Faruk da Abirma.

Laftanal Kanal Uba Sani ya ce dakarun sun samu taimako daga bangaren sojin saman Rundunar Operation Hadin Kai da suka taimaka da bayanan sirri da kuma sanya ido a gaba daya lokacin da aka kai farmakin.

Sojojin saman sun rika bin sahun ’yan ta’addan da kuma dakile duk wani taimako da za su iya samu da kuma bayar da bayanan da za su taimaka wajen samun nasarar farmakin. Sannan da karfafa wa dakarun da ke kasa gwiwa.

Ya ce bayan farmakin sojojin Nijeriya sun yi nasarar gano harsasai da wayoyi da tutocin ’yan Boko Haram da man dizal da magunguna masu yawa da buhunhunan hatsi da a-kori-kura da wajen boye man fetur da wanda yake karkashin kasa da sauransu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#