Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bayan samun rahoton dai, gwamnan jihar Kaduna ya kira taron majalisar Tsaro ta Jiha.

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta yi amai ta lashe kan musanta garkuwa da mutane a Kaduna

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana irin rudanin da jama'a suka shiga bayan samun rahotannin garkuwa da mutane a kauyen Kurmin Wali da ke karamar Hukumar Jihar Kaduna, in ji wata sanarwa da aka fitar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Kakakin Rundunar na Kasa CSP Benjamin Hundeyin, ta ce rundunar ta fahimci irin tsoro da fargabar da iyalan mutanen, mazauna yankin da al’umma gaba daya ke da ita, kuma da dauki zaman lafiyar kowa da matukar muhimmanci.

Bayan samun rahoton dai, gwamnan jihar Kaduna ya kira taron majalisar Tsaro ta Jiha.

A yayin zaman a fadar gwamnatin Kaduna, wasu mahalarta daga yankin sun musanta labarin, wanda tun da fari ‘yan sanda sun tabbatatr da kanzon kurege ne. Hakan ya sanya rashin tabbas da kawo bukatar dole a yi bincike da tantancewa kafin a fito bainar jama’a a bayar da wata sanarwa.

Bayan wani zuzzurfan bincike da aka gudanar, rundunar ta tabbatar da an yi garkuwa da mutanen.

Saboda haka, tuni rundunar ‘yansandan ta Nijeriya ta bazama tare da hada hannu da sauran jami’an tsaro don ganin an kubutar da mutanen cikin koshin lafiya.

Supetan ‘yansandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin aika jami’an tsaro da kayan leken asiri don gano wa da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta kuma ce rundunar ta bukaci jama’a da ‘yan jaridu da su yi hakuri tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.

Rahotannin da aka samu sun ce a ranar Lahadi ne ‘yan ta’adda suka yi tururuwa zuwa yankin tare da garkuwa da mutum 160 da ke bauta a cocina daban-daban a ranar Lahadi 18 ga Janairu.

Amma Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN ta bayyana wa manema labarai cewa an yi garkuwa da mutane 172, amma 9 daga cikin sun kubuta. yayin dakaka tisa keyar sauran zuwa dazukan yankin.

Sanarwar da kakakin kungiyar a Kaduna Ruben Buhari ya fitar ta lissafo cocinan da lamarin ya rutsa da su da suka hada da cocinECWA, Albarka Cherubim da Seraphim 1 da Haske Cherubim da Seraphim 2.

Jihar Kaduna da ke arewa maso-yammacin Nijeriya na fama da rikicin ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#