Sport
Dollar
38,8949
0.36 %Euro
43,4533
-0.25 %Gram Gold
3.997,1000
-0.9 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce sabuwar rijiyar mai ɗauke da cubic meter biliyan 75 na gas, za ta iya wadata gidaje a ƙasar da gas tsawon shekara uku da rabi.
Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya sanar da gano sabuwar rijiyar iskar gas mai ɗauke da cubic meter biliyan 75 na gas ɗin a Tekun Bahar Aswad.
“Mun gano sabuwar rijiyar gas mai ɗauke da cubic meter biliyan 75 a wannan filin. Tare da wannan adadin, za mu iya biyan bukatun gidaje kawai na kusan shekaru 3.5,” in ji Erdogan yayin jawabinsa a wajen bude Asibitin Horarwa da Bincike a Istanbul.
“Aikinmu a rijiyar Goktepe-3 (a cikin Bahar Aswad), wanda muka fara a ranar 27 ga Maris tare da jirgin hakar mai na zamani na Abdulhamid Han, ya kammala daga jiya,” in ji shi.
Erdogan ya jaddada kudurin Ankara na samun 'yancin kai a fannin makamashi.
“Za mu ci gaba da tafiya ba tare da tsayawa ba, ba tare da hutawa ba, kuma ba tare da kula da suka ko cikas ba har sai mun cim ma burinmu na samun cikakken 'yancin kai a fannin makamashi,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
A kan hanyar samun 'yancin kai a fannin makamashi
A cikin 'yan shekarun nan, Turkiyya ta sanar da gano babbar rijiyar iskar gas a cikin Bahar Aswad, wadda aka kiyasta tana da cubic meter biliyan 710. A halin yanzu, samar da iskar gas a cikin gida yana biyan buƙatun kusan kashi 7 zuwa 8 cikin 100 na buƙatar da ake da ita a ƙasar, wanda ke zama mataki mai muhimmanci wajen samun 'yancin kai a fannin makamashi da rage dogaro da shigo da kaya.
Haka kuma, ƙasar tana ci gaba da ɗaukar matakai na gaba don tabbatar da makomar makamashinta tare da kulla manyan yarjejeniyoyin LNG guda biyu a wannan watan, wanda ke ƙarfafa burinta na zama cibiyar makamashi a yankin.
Comments
No comments Yet
Comment