Sport
Jami’an Iran da Amurka sun nuna alamun samun ci gaba a tattaunawar nukiliya inda ska amince cewa akwai yiwuwar ci gaba da tattaunawa nan gaba a Muscat da ke Oman.
Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka , wadda aka yi da taimakon ƙasashen yanki, ta nuna alamun “ci-gaba,” kamar yadda Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana ranar Lahadi.
“Tun da can tattaunawa ita ce dabararmu ta samun mafita ta lumana ,” kamar yadda Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na shafin sada zumunta na X, yana mai jaddada cewa hanyar da Iran ta bi kan batun nukiliya ta dogara ne kan “‘yancin da aka tabbatar a yarjejeniyar hana yaɗuwar makamin nukiliya.”
Shugaban na Iran ya ƙara da cewa ƙasar “tana mayar da martani ga girmamawa da ladabi, amma ba ta lamuntar kalaman tilastawa.”
Iran da Amurka sun soma harkar diflomasiyyar nukiliya a kaikaice ranar Juma’a bayan makonni na tashin hankali, wanda barzanar matakin sojin Shugaban Amurka Donald Trump kan ƙasar ta yi ta yi.
Minsitan Harkokin Waje Abbas Araghchi ya bayyana tattaunawar a matsayin wani “mafari mai kyau,” yana mai cewa za su iya ci gaba idan aka shawo kan yanayin rashin aminci.
Ya ce an amince cewa za a ci da bin matakin da kuma cewa ɓangarorin biyu za su sake haɗuwa a Muscat, Oman, nan gaba.
Araghchi ya bayyana cewa shirin makami mai linzamin Iran ba zai kasance ƙarƙshin ko wace tattaunawa ba a yanzu ko kuma a nan gaba, yana mai bayyana shi a matsayin “harkar tsaro.”
Comments
No comments Yet
Comment