Erdogan da MBS sun yi Allah wadai da duk wani yunƙurin raba ƙasashe a yankin

Turkiyya da Saudiyya sun goyi bayan haɗin kan Somaliya, Sudan da Yemen

Turkiyya da Saudiyya sun jaddada cikakken goyon bayansu ga iko, ‘yanci da haɗin kan Somaliya, inda suka yi watsi da duk wani yunƙuri da ke barazana ga dunkulewar ƙasar a yankin Kusurwar Afirka. Wannan matsaya ta fito ne bayan ganawar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a Riyadh. TRT Hausa

Ƙasashen biyu sun yi Allah wadai da yarjejeniyar amincewa da juna tsakanin Isra’ila da yankin Somaliland, suna masu cewa hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa tare da ƙarfafa yunƙurin raba Somaliya. Sun jaddada cewa Somaliland muhimmin ɓangare ne na Somaliya duk da ayyana kanta a matsayin mai cin gashin kai tun 1991. TRT Hausa

A batun Yemen, Ankara da Riyadh sun tabbatar da goyon bayansu ga halastacciyar gwamnatin ƙasar, tare da nuna muhimmancin kare iko, haɗin kai da ‘yancin Yemen. Turkiyya ta yaba da rawar da Saudiyya ke takawa wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin da kuma sulhu tsakanin ɓangarorin Yemen. TRT Hausa

Game da Sudan, Turkiyya da Saudiyya sun jaddada tsayuwarsu kan kiyaye haɗin kan ƙasar, tsaro da ‘yancinta, tare da yin kira da a kare fararen-hula da tabbatar da isar da agajin jinƙai ba tare da tangarda ba. Sun kuma yi watsi da duk wani tsari da ba ya bisa doka a ƙasar. TRT Hausa

A kan Syria, shugabannin biyu sun yi kira da Isra’ila ta janye daga dukkan yankunan Syria da ta mamaye, suna masu cewa hare-haren Isra’ila na take ikon ƙasar tare da barazana ga zaman lafiya a yankin. Sun kuma goyi bayan ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali da ɗage takunkumi kan Damascus. TRT Hausa

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#