Dollar

42,3350

0.2 %

Euro

49,1712

0.05 %

Gram Gold

5.547,4900

-0.07 %

Quarter Gold

9.430,0100

0 %

Silver

69,2000

0.51 %

Senegal ta tabbatar da isar Shugaba Embalo Dakar "cikin ƙoshin lafiya " bayan juyin mulki ya hana fitar da sakamakon zaɓe a Guinea-Bissau.

Shugaban Guinea-Bissau ya tsere zuwa Senegal bayan sojoji sun yi masa juyin mulki

Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya isa Senegal bayan an tsare shi, a wani juyin mulkin sojoji a ƙasarsa, kamar yadda gwamnatin Senegal ta bayyana ranar Alhamis.

“Gwamnati ta ɗau hayar wani jirgin sama domin ya je Bissau domin taimakawa wajen aikin dawo da mutane. Wannan ya ba da damar isowar Shugaba Umaro Sissoco Embalo Snegal cikin ƙoshin lafiya,” kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Senegal ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar.

Rundunar sojin Guinea-Bissau ta naɗa wani janar a matsayin sabon shugaban ƙasar ranar Alhamis, kwana ɗaya bayan karɓe mulki da kuma dakatar da fitar da sakamakon zaɓe.

Dan takarar jam’iyyar hamayya Fernando Dias da Costa ya shaida wa AFP cewa ya yi imanin shi ya ci zaɓen na ranar Lahadi, kuma ya yi zargin cewa Embalo — wanda ya yi iƙirarin nasara — ya "shirya" juyin mulkin domin hana shi karɓar ragamar mulkin.

Juyin mulkin ya zo ne kwana ɗaya kafin a fara fitar da sakamakon zaɓen na farko-farko na shugabna ƙasa da na ‘yan majalisu.

Janar Horta N’Tam, babban hafsan sojin ƙasan ƙasar, shi aka ayyana a matsayin shugaba na shekara ɗaya.

Ya sha rantsuwa a hedikwatar sojoji, in da ya bayyana cewa: "Yanzun nan aka rantsar da ni domin na jagoranci babbar runduna [ta mulki]."

ECOWAS ta dakatar da Guinea-Bissau

Shugabannin Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka Ta Yamma ECOWAS sun dakatar da Guinea-Bissau ranar Alhamis daga dukkanin hukumominta na yanke shawara bayan juyin mulkin, in ji wata sanarwa da ta biyo bayan wani taro na gaggawa.

Ƙungiyar ta kuma soki juyin mulkin inda ta yi kira ga shugabannin juyin mulkin su bai wa hukumar zaɓen ƙasar damar fitar da sakamakon zaɓen da ake cece-ku-ce a kai.

Ɗan takaran jam’iyyar adawa ya kuɓuce daga kame

Ana ganin N’Tam yana ƙara zama na hannun daman Embalo cikin ‘yan shekarunnan.

Dias, da yake magana ta waya daga inda yake ɓuya, ya yi iƙirarin cewa: "Ni ne shugaban ƙasa (da aka zaɓa) na Guinea-Bissau," kuma ya ce shi ya yi imanin cewa shi ya lashi kashi 52 cikin 100 na ƙuri’u.

"Ba wani juyin mulki," kamar yadda ya yi iƙirari. "Mista Embalo ne ya shirya shi."

Ya ce shi ya tsere ne daga hedikwatar yaƙin naman ranar laraba lokacin da mutane ɗauke da makamai suka yi ƙoƙarin kama shi.

An kama Domingos Simoes Pereira, babban ɗan adawan da aka hana tsayawa takara kuma daga baya ya mara wa Dias baya, a ranara Laraba.

Rundunar sojin ta kuma naɗa Janar Tomas Djassi, wanda a baya shugaban ma’aikatan Embalo ne, a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa na ƙsar.

 

Soji ta matsa kaimi kan iko

Guinea-Bissau ta tsaya cak ranar Alhami, inda aka rufe shaguna kuma sojoji suke sintiri kan hanyoyi.

Sabbin shugabanni na sojin sun hanya watsa shirye-shirye na kafofin watsa labarai tare da hana zanga-zanga.

Yayin da sojoji masu riƙe da makamai suka kewaye shi, N’Tam ya shaida wa manema labarai cewa sojin ta ɗauki matkin ne "domin toshe ayyukan da ke ƙoƙarin yin barzana ga Dimokraɗiyya."

Y ace hujjoji sun "isa tabbatar da cewa [gaskiyar] aikin " kuma yi kira ga ƙsa ta taka rawa wajen "matakan da ake buƙata."

Kan iyakoki, wadanda aka rufe ranar Laraba, an buɗe su daga baya, kuma aka ɗaga dokar hana fita.

Rundunar mulkin sojin ta ba da umarnin sake buɗe kasuwanni da makaranti da da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Ƙungiyar tarayyar Afirka ta soki juyin mulkin kuma ta nemi a sake Embalo nan take, yayin da shugaban ECOWAS Julius Maada Bio ya bayyan shi a matsayin "mummunan ƙeta tsarin mulkin Guinea-Bissau."

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi kira da ƙasar ta koma tafarkin Dimokraɗiyya cikin gaggawa.

Guinea-Bissau ta fuskanci juyin mulki da dama tun lokacin da ta sami ‘yancin kai a shekarar 1974, kuma ana yawan musanta sakamakon zaɓukanta.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#