Sport
Dollar
42,3350
0.2 %Euro
49,1712
0.05 %Gram Gold
5.547,4900
-0.07 %Quarter Gold
9.430,0100
0 %Silver
69,2000
0.51 %Tun da fari hukumar zabe ta gargaɗi masu zaɓe, da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, da ƙungiyoyin zaɓe da kuma kafofin watsa labarai game da sanar da yin taka tsan-tsan wajen sanar da duk wani sakamako.
An yi ta jin karar harbe-harbe kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau a ranar Laraba yayin da rikici ya kaure bayan zaben Shugaban Ƙasa da aka gudanar, inda 'yan takara biyu kowannensu ya ayyana samun nasara na lashe zaben, a cewar kafofin watsa labaran Faransa.
Kazallika, kafofin yada labarai na cikin gida a Gunea- Bissau sun kuma tabbatar da rahoton cewa "a daidai wannan lokacin, za ku iya jin ƙarar harbe-harbe a Bissau, ƙarar na fitowa ne daga Fadar Shugaban Ƙasa," a cewar rahoton Bantaba Radio/TV.
A ranar Litinin ne Fernando Dias, ɗan takara mai zaman kansa, da kuma magoya bayan Shugaba Umaro Sissoco Embalo suka yi ikirarin lashe zaben Shugaban Ƙasa na Guinea-Bissau da aka gudanar a ƙarshen mako yayin da al’ummar ƙasar ke jiran sakamakon.
Hukumar zaɓen ƙasar ta yi alƙawarin sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen nan da ranar Alhamis.
Hukumar ta gargaɗi masu zaɓe, da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, da ƙungiyoyin zaɓe da kuma kafofin watsa labarai game da sanar da yin taka tsan-tsan wajen sanar da duk wani sakamako.
Jakadan Ghana Baba Kamara, wanda kuma shi ne shugaban tawagar sa ido kan zaɓen daga Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a Guinea-Bissau a babban zaɓen da aka gudanar a ranar 23 ga Nuwamba, ya ce tsarin zaɓen ya tafi daidai.
'Yan takara goma sha biyu ne suka fafata a takarar neman kujerar shugaban ƙasa.
Tun lokacin da shugaban Embalo ya hau karagar mulki a shekarar 2020, an yi ta samu rahotanni da dama na yunƙurin juyin mulki, wani al’amari da ke nuna rirn mummunar adawa da yake fuskanta.
Comments
No comments Yet
Comment