Sport
Dollar
40,6834
0.04 %Euro
47,6866
0.3 %Gram Gold
4.417,1900
0.32 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A ƙasar Ghana, an taya kantunan kamfanin bakwai da kuma ɗakin ajiya ɗaya a watan Yuni. Yiwuwar cinikin ya faɗa na da ƙarfi sosai, in ji Shoprite.
Kamfanin sayar da kayayyakin abinci mafi girma na Afirka ta Kudu, Shoprite Holdings, ya bayyana ranar Talata cewa zai sayar da kantunansa a Ghana da Malawi, a wani mataki na haɗa kan hajojinsa a Afirka domin mayar da hankali kan kasuwar cikin gida.
Kantin na Shoprite ya faɗaɗa harkokinsa matuƙa a faɗin Afirka, lamarin da ya sa ya zarce kishiyoyinsa kamar su Pick n Pay da Massmart wajen kasancewa kantin sayar da kayayyakin abinci da ke kan gaba a nahiyar cikin kimanin ƙasashe 15.
Amma shigarsa kasuwanni irin su Angola da Nijeriya ta yi fama da rashin daidaituwar kuɗi da hauhawar farashi da tsadar harajin shigar da kaya da kuma kuɗin haya da ake biya da dala, in ji kamfanin dillancin labaran Reuters.
Ranar Talata ya ruwaito cewa reshen kamfanin Shoprite na Malawi ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ranar 6 ga watan Yuni domin sayar da kantunansa biyar har zuwa lokacin da aka cika wasu sharuɗɗa ciki har da samun dama daga hukumar da ke sa ido kan gogayya a kasuwanci da kuma babban bankin Malawi.
A ƙasar Ghana, an taya kantunan kamfanin bakwai da kuma ɗakin ajiya ɗaya a watan Yuni. Yiwuwar cinikin ya faɗa na da ƙarfi sosai, in ji Shoprite.
Zuwa dai ƙarfe 07:53 agogon GMT hannayen jarin kamfanin sun faɗi da kashi 2.60 cikin 100.
Shirin sayar da shagunan na zuwa ne bayan kamfanin ya fice daga Nijeriya da Kenya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Yuganda da Madagascar. Shoprite ya kuma taƙaita ware jari ga kantunasa da ke wajen ƙasar Afirka ta Kudu.
Comments
No comments Yet
Comment