Dollar

40,7086

0.17 %

Euro

47,4348

-0.19 %

Gram Gold

4.444,4400

0.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Samo ƙarin labarai da ƙarin haske daga TRT Global cikin harsuna 45. Sun haɗa da batutuwa na duniya siyasa kasuwanci wasanni da sauransu.

Nijar za ta sayo na'urori tare da gina sashen gwajin ciwon daji kan dala miliyan biyu

Gwamnatin ƙasar Nijar za ta gina ɓangaren gwajin ciwon daji tare da sayen na’urorin gwajin ciwon daji kan dala miliyan 2,300,000 wato Sefa sama da biliyan 13.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar (ANP) ya ruwaito cewa shugaban ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ne ya ƙaddamar da bikin aza tubalin ginin sashen gwajin ciwon dajin a asibitin ƙwararru na Yamai ranar Litinin.

Bayan ya gama aza tubalin, Shugaba Tiani ya ce ɓangaren zai ba da damar gano ciwon daji da wuri da kuma ɗaukar mataki a kansa.

Shugabna ya kuma gode wa ma’aikatan jinyan ƙasar da ma ‘yan ƙasar baki ɗaya game haɗin kansu.

A nasa jawabin, ministan ma’aikatar lafiya ta ƙasar, Kanal-Manjo Garba Hakimi ya bayyana cewa "Nijar, wajen aiwatar da tsarin yaƙar cututtuka mara yaɗuwa ciki har da ciwon daji, tana nuna jajircewarta wajen rage tasirinsu kan ingancin rayuwar mutane."

Ministan ya ce na’urar wadda ita ce ta farko a yankin za ta taimaka wajen gudanar da ingantaccen gwajin ciwon daji.

Da yake magan game da yadda za a samar da kuɗin aikin, Garba Hakimi ya ce ƙasar za ta samu kuɗin ginin da na’urar (dala miliyan 2,3000,000) ta hanyar yarjejenkiya da hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA).

Da zaran an kammala aikin, na’urar za ta taimaka wajen iya gano ciwon daji  a asibitin ƙwararru na Yamai ta hanya mafi ingancin da zai ba da damar iya yi wa mara lafiya maganin da ya dace, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#