Dollar

40,7086

0.17 %

Euro

47,4348

-0.19 %

Gram Gold

4.444,4400

0.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Gwamnatocin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar da maƙotansu Burkina Faso da Mali sun matsa lamba kan kamfanonin haƙar ma'adanai na ƙasashen waje a shekarun baya bayan na, inda Nijar ta ƙwace kamfanin haƙar yuraniyom na Faransa, Orano a watan Yuni.

Gwamnatin Nijar ta ƙwace mahaƙar zinari daga kamfanin Australia

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙwace mahaƙar zinari ɗaya tilo a ƙasar, bayan da ta zargi kamfanin Australia da ke gudanar da ita da "manyan laifukan keta doka" a yayin da gwamnatin take neman karɓe ragamar harkokin ma’adanai na ƙasar.

Gwamnatin soji, wadda ta ƙwace mulki daga gwamnatin farar-hula a shekarar 2023, ta sha alwashin magance rashin tsaro da ya addabi ƙsar.

Kamfanin McKinel Resources Limited na Australia ta amshi ragamar gudanar da haƙar zinari ta Societe des mines du Liptako (SML), wadda ke Kogin Neja a 2019 bayan ta sayi kaso mafi tsoka daga wurin gwamnati.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#