Sport
Dollar
40,7086
0.17 %Euro
47,4348
-0.19 %Gram Gold
4.444,4400
0.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A ‘yan shekarun baya-bayan nan, kasar Rwanda ta sanya kanta a matsayin kasar da kasashen yammacin duniya za su iya koro baƙin haure.
Amurka da Rwanda sun amince kasar wadda ke yankin Afirka ta karbi bakin haure 250 da aka kora daga Amurka, kamar yadda kakakin gwamnatin Rwanda da wani jami'in kasar suka bayyana.
"Rwanda ta amince wa Amurka kan za ta karbi bakin haure kusan 250, saboda kusan kowane iyali a Ruwanda sun taɓa fuskantar wahalhalun rasa matsuguni, kuma al'ummarmu sun ginu ne a kan karban baki cikin al’umma da kuma ba su matsuguni," a cewar mai magana da yawun gwamnatin Rwanda, Yolande Makolo.
"A karkashin yarjejeniyar da aka cim ma, Rwanda na da ikon karbar kowane mutum da aka nemi sake tsugunarwa. Za a ba wadanda aka amince da zamansu horo na aiki, da kulawa ta lafiya da tallafin masauki don fara rayuwa a Rwanda, yanayin da zai ba ba su damar ba da gudummawa a daya daga cikin kasashe masu tasowa cikin sauri a tattalin arziki na duniya," in ji ta.
Jami'an Amurka da na Rwanda ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Kigali a watan Yuni kuma tuni Washington ta aika da jerin sunayen mutane 10 na farko da za a tantance, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Kasa ta uku da ake kora baƙin-haure
Shugaba Donald Trump na da nufin korar miliyoyin baƙin haure a Amurka ba bisa ka'ida ba, kuma gwamnatinsa ta kuduri aniyyar aika baƙin zuwa kasashe uku, ciki har da tura masu laifi zuwa Sudan ta Kudu da Eswatini, wadda a baya ake kira Swaziland.
A ‘yan shekarun baya-bayan nan, kasar Rwanda ta sanya kanta a matsayin kasar da kasashen yammacin duniya za su iya koro baƙin haure.
A cikin watan Mayu ne, ministan harkokin wajen kasar ya ce Rwanda tana tattaunawa kan shirin karbar baƙin haure da aka kora daga Amurka.
Gwamnatin Trump ta kafa hujja kan cewa, samun kasa ta uku da za a kora baƙin- haure za ta taimaka wajen rage fitar da su, sai dai ‘yan adawa sun soki matakin, inda suka ce yin hakan rashin tausayi ne kuma yana da haɗari, la’akari da cewa za a tura mutane zuwa kasashen da ba su da wata alaka kuma ba sa jin yaren.
A watan Yuni ne kotun koli ta bai wa gwamnatin Trump damar tasa keyar bakin-haure zuwa kasashe uku ba tare da ba su damar nuna cewa za a iya cutar da su ba.
Tattalin arziki da ke bunƙasa
Shugabannin kasashen yammacin duniya da na shiyya-shiyya sun yabawa shugaba Paul Kagame kan sauya kasar Rwanda daga koma bayan kisan kare dangi na shekarar 1994 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da miliyan daya zuwa ga kasar da tattalin arziki ke bunƙasa.
Kazalika Rwanda ta shiga tattaunawar zaman lafiya karkashin jagorancin gwamnatin Trump domin kawo karshen faɗa a gabashin Kongo. Kasashen Afirka biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka a watan Yuni a birnin Washington, lamarin da ke kara sanya fatan kawo karshen yakin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu dabbai da matsugunansu.
Comments
No comments Yet
Comment