An buga : 7 Maris 2026
Sabuntawa : 7 Maris 2026
Shugaba Mahama ya rantsar da shi tare da kira ga kare ‘yancin ɓangaren shari’a
Maishari’a Paul Baffoe-Bonnie ya kama aiki a matsayin sabon Alƙalin Alƙalan ƙasar Ghana na tara tun bayan da ƙasar ta fara jamhuriya ta huɗu.
Shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ne ya rantsar da shi a fadar gwamnatin ƙasar da ke Accra a ranar Litinin, a wani biki da ya samu halartar alƙalan manyan kotuna, ‘yan majalisar dokoki da manyan jami’an gwamnati tare da ‘yan uwansa.
Majalisar dokokin ƙasar ta amince da sunansa a ranar Alhamis bayan da Shugaban ƙasar ya miƙa sunansa domin naɗa shi a matsayin sabon Alƙalin Alƙalan ƙasar.
Kafin rantsar da shi, Maishari’a Baffoe-Bonnie yana aiki ne a matsayin muƙaddashin Alƙalin Alƙalan ƙasar tun daga ranar 22 ga watan Afrilu na shekarar 2025.
Yayin da yake rantsar da shi, Shugaba Mahama ya bukaci sabon Alƙalin Alƙalan da ya gudanar da aikinsa bisa gaskiya, adalci da kuma ‘yancin kai kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1992 ya tanada.
Shugaban ya bayyana cewa ƙarfin dimokraɗiyyar Ghana na dogara ne da daidaiton iko tsakanin ɓangarorin gwamnati uku wato ɓangaren zartarwa da na dokoki da kuma na shari’a.
Ya ƙara da cewa dukkan waɗannan ɓangarori dole ne su yi aiki cikin ‘yanci amma kuma cikin haɗin kai domin tabbatar da jin daɗin al’ummar ƙasar.
Mahama ya kuma jaddada aniyarsa ta kare ‘yancin ɓangaren shari’a, yana mai cewa tsarin shari’a mai ‘yanci muhimmin ginshiƙi ne na kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa har da shugaban ƙasa.
Haka kuma ya yi kira ga sabon Alƙalin Alƙalan da ya gudanar da aikinsa ba tare da son rai ko wariya ba, yana mai gargadin cewa duk wani zargi na cin hanci daga jami’an shari’a na iya lalata amincewar jama’a da tsarin gaba ɗaya.
Tushen labari: Newstimehub
Erdogan na Turkiyya: 'Babu wata damar rarrabuwar kai a duniyar Turkawa'
Shugaban Turkiyya Erdogan ya ce taron na Ankara zai ƙarfafa hadin kai,inda Turkiyya ta shirya domin kasancewa shugabar Ƙungiyar Ƙasashen Turkawa.
Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan DAESH 48, sun ƙwato makamai a jihohin Borno da Yobe
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a, rundunar ta ce dakarunta sun dakile wani yunƙurin kai hari kan sansanin soji da ke Bitta, a ƙaramar hukumar Gwoza ta Jihar Borno, a daren ranar 29 ga Oktoba.
Tinubu ya kare matakin karɓo bashi daga waje, ya ce Nijeriya na buƙatar haɓaka tattalin arziki
Kalaman shugaban ƙasar na zuwa ne a cikin sukar matakin gwamnatin na aron kuɗaɗe da kuma tasirin hakan ga nauyin bashi kan ƙasar.
Yawancin Karatu