Dollar

41,9875

0.02 %

Euro

48,6811

-0.1 %

Gram Gold

5.502,2400

-1.17 %

Quarter Gold

9.708,1700

-2.27 %

Silver

65,5300

-0.37 %

Kocin Al-Nassr ta Saudiyya ya ce Cristiano Ronaldo bai yi tafiya da 'yan wasan ƙungiyar ba zuwa India don buga wasan Gasar Zakarun Asiya tare da ƙungiyar Goa.

Ronaldo ba zai je India buga wasan Al-Nassr da Goa ba

Kocin Al-Nassr ta Saudiyya, Jorge Jesus ya faɗi dalilin rashin tafiya India da Cristiano Ronaldo don buga wasa da ƙungiyar Goa ta India.

Wasan na Gasar Zakarun Asiya, za a buga shi ne ranar Laraba 21 ga Oktoba a filin wasa na Fatorda da ke garin Goa.

Mai shekaru 40, Ronaldo ya ci ƙwallaye 5 zuwa yanzu a wasanni 5, ciki har da wata ƙwallon da ya ci Al-Fateh bayan ya zubar da bugun ɗurme a gasar Saudi Pro ranar 18 ga Oktoba.

Al-Nassr dai tana da wasu zaratan ‘yan wasan gaba, kamar Sadio Mane, da Kingsley Coman, da Joao Felix, waɗanda za su taimaka wajen fitar da ita kunya a India.

Sai dai masoya Ronaldo da ke ƙasar India da suka yi fatan yin tozali da shi, sun ji takaicin rashin zuwan gwarzon ɗan ƙwallon.

Da aka tambayi kocin Al-Nassr, Jorge Jesus game da rashin halartar Ronaldo, ya ce batu ne kawai na rage wa tauraron ɗanwasan aiki.

Jesus ya ce, "Kowa na son ganin Cristiano Ronaldo, kuma yana da tarin masoya. Mun yanke hukuncin mu bar shi ya huta a wasanmu na wajen Saudiyya.”

A kwanakin nan, Ronaldo yana tashen cin ƙwallo a ƙungiyar tasa, da kuma ƙasarsa Portugal a wasannin neman cancantar buga gasar kofin duniya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#