Dollar

40,9482

0.01 %

Euro

47,6960

-0.17 %

Gram Gold

4.393,7100

-0.3 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Rikicin ya ɓarke ne bayan Ooni na Ife ya naɗa wani ɗankasuwa, Jubril Dotun Sanusi, sarautar Okanlomo na ƙasar Yarbawa

Rikici ya kunno kai tsakanin Sarakunan Oyo da Ife a kan ikon naɗin sarauta a ƙasar Yarabawa

Wani rikicin cacar baka ya ɓarke tsakanin Alaafin na Oyo, Oba Ayoade Akeem Oweye da kuma Ooni na Ile Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi a kan ikon naɗin sarauta a garuruwan Yarabawa.

Rikicin ya ɓarke ne bayan Ooni na Ife ya naɗa wani ɗan kasuwa, Jubril Dotun Sanusi sarautar Okanlomo na ƙasar Yarabawa

Bayan Ooni ya naɗa ɗan kasuwan ne dai Alaafin na Oyo ya bai wa Ooni wa’adin sa’o’i 48 ya janye sarautar yana mai cewa Ooni ba shi da ikon naɗin sarautar da ta shafi ƙasar Yarabawa gaba ɗaya.

Wata sanarwar da sakataren watsa labaran Alaafin na Oyo, Bode Durojaye ya fitar ta ce naɗin da Ooni ya yi na ƙalubalantar ikon Alaafin ne kai tsaye.

Sanarwar ta ƙara da cewa Alaafin na Oyo ne kawai yake da ikon naɗin sarautar da ta shafi duk ƙasar Yarabawa a Nijeriya.

“Kotun Ƙoli kanta ta yanke hukuncin cewa Alaafin ne kawai yake da irin wannan ikon [na naɗin irin wannan sarautar]. Duk da haka, Ooni ya ci gaba da bijire wa doka, yana mai take al’ada da umarnin kotuna,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce idan Ooni bai janye sarautar cikin sa’o’i 48 ba, zai ga abin da zai biyo baya.

Shi kuwa sakataren watsa labarai na Ooni na Ife, Moses Olafare ya ce Ooni ya hana shi fitar da sanarwa a matsayin martani kan gargaɗin da Alaafin ya yi.

“Shugabana ya ba ni umarnin ka da na fitar da sanarwa kan fankon gargaɗin. Na roƙi gafararku ‘yan jarida masu mutunci,” kamar yadda jaridun ƙasar suka ambato Olafare yana cewe a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#