Sport
Dollar
40,9427
0.01 %Euro
47,6482
-0.18 %Gram Gold
4.395,1500
-0.27 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kwamishinan Watsa Labarai na Kano Ibrahim Abdullahi-Waiya ya ce gwamnan ya nuna matuƙar damuwa dangane da yadda harkar daba ke ƙara ƙaruwa a jihar inda ya ce lamarin na ƙara ƙazanta kuma yana ɓata wa jihar suna.
A wani sabon mataki na magance ta’addancin siyasa da tashin hankali tsakanin matasa, Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna “Safe Corridor” na yin afuwa da farfaɗo da rayuwar matasan da suka tuba daga munanan ɗabi’u waɗanda suka haɗa da harkar daba a jihar.
Gwamna jihar Abba Kabir Yusuf ya fito da wannan tsarin ne da nufi rage barazanar da ƙungiyoyin matasa masu tayar da rikici ke yi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan daban suka addabi jama’ar jihar musamman da ƙwacen wayoyi da kuma kashe waɗanda suke ƙwace wa wayoyin a wasu lokutan.
Kwamishinan Watsa Labarai na Kano Ibrahim Abdullahi-Waiya ya ce gwamnan ya nuna matuƙar damuwa dangane da yadda harkar daba ke ƙara ƙaruwa a jihar inda ya ce lamarin na ƙara ƙazanta kuma yana ɓata wa jihar suna.
A shirye-shiryen gwamnatin na afuwa, tuni aka tantance matasa 718, yayin da wasu 960 ke jiran tantancewa daga rundunar ’yan sanda kafin a haɗa su cikin shirin.
Tsarin tantancewar ya haɗa da binciken tsaro daga ’yan sanda, gwajin miyagun ƙwayoyi daga hukumar NDLEA, sannan daga nan za a shiga matakin gyara hali da sake haɗa su cikin al’umma.
Me waɗanda suka tuba za su amfana da shi?
Babban tagomashin da waɗanda suka tuba za su samu daga gwamnatin jihar shi ne afuwa.
Wannan na nufin za a yafe musu duka laifuffukansu sannan kuma a ba su dama domin rayuwa a matsayin ‘yan ƙasa masu bin doka.
Gwamnati ta kuma yi alƙawarin samar da ayyukan yi, sana’o’in dogaro da kai da kuma tallafin ga tubabbun domin ƙarfafa musu gwiwa wajen sake gina rayuwarsu.
Comments
No comments Yet
Comment