Sport
Dollar
40,9443
0.02 %Euro
47,7093
-0.14 %Gram Gold
4.394,1400
-0.29 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Mai Shari’a Emeka Nwite ya ba da wannan umarnin ne ranar Talata bayan lauyar hukumar, Ogechi Ujam, ta nemi kotun ta hana amfani da asusun bankin guda huɗu.
Babbar kotun Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ke Abuja ta ba da umarnin hana amfani na wucin-gadi da asusun banki huɗu da ke da alaƙa da tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya, NNPCL, Mele Kyari bisa zarge-zargen almundahana.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin ne ranar Talata bayan lauyar hukumar EFCC, Ogechi Ujam, ta nemi kotun ta hana amfani da asusun guda huɗu na bankin Jaiz zuwa lokacin da hukumar za ta kammala bincike.
Alƙalin, a hukuncin da ya yanke, ya ce EFCC tana da hujja mai ƙwari, saboda haka ya amince da buƙatarta.
“Na saurari lauyar mai neman ɗaukar matakin kuma na duba hujjoji da bayanan da aka haɗa da buƙatar, na gane cewa buƙatar tana da ƙwaƙƙwarar hujja, kuma yanzu na ba da izinin aiwatar da ita,” in ji alƙalin.
Kana Mai Shari’a Nwite ya ɗage zaman kotun zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin jin ba’asin wani rahoto game da batun.
Ranar 11 ga watan Agustan shekarar 2025 ne hukumar EFCC ta gabatar da buƙatar neman kotun ta hana amfani da asusun bankin na Kyari, “wanda ake gudanar da bincike a kansa a halin yanzu game da wani batu na laifukan haɗa baki da amfani da ofishinsa ta hanyar da bata dace ba da kuma halatta kuɗin haram zuwa lokacin da za a kammala bincike.”
A jikin wata takardar rantsuwa da ya haɗa da buƙatar, Amin Abdullahi, wani mai bincike a hukumar EFCC, ya ce a ranar 24 ga watan Afrilu ne wata ƙungiya ta kai ƙarar Kyari hukumar kana hukumar ta yi bincike kan ƙarar.
Ya ce shi kansa yana cikin waɗanda aka bai wa aikin bincike game da ƙarar.
“Daga samun takardar ƙarar da muka nuna a sakin layi na huɗu, tawagata ta yi ayyukan bincike ciki har da neman bayanai daga bankuna,” in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment