Sport
Dollar
41,1664
0.01 %Euro
48,0522
0.03 %Gram Gold
4.686,2900
-0.52 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%“Sabon tsarin zai kawo daidaito a darussan da ake koyarwa wajen zurfafawa da kuma koyar da ilimi a aikace.
Gwamnatin Nijeriya ta kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha, da nufin rage lafta karatu da kuma inganta tsarin koyarwa.
Sabuwar manhajar za ta fara ne a wannan shekarar karatun ta 2025/2026.
Da take sanar da matakin a madadin Ministan Ilimi Dakta Maruf Tunji Alausa, Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, ta ce an gudanar da bitar ne tare da hadin gwiwar Hukumar Bincike da Cigaban Ilimi ta Nijeriya (NERDC), da hukumar ilimin bai-ɗaya a matakin farko Universal Basic Education Council UBEC, da NSSEC, da NBTE, da sauran masu ruwa da tsaki.
“Sabon tsarin zai kawo daidaito a darussan da ake koyarwa wajen zurfafawa da kuma koyar da ilimi a aikace.
Comments
No comments Yet
Comment