Hukumar ta kuma yi nasarar samun mutum 89 da laifi da kuma shigar da sabbin ƙara 126 gaban kotu a cikin watanni tara, yayin da ake ci gaba da shari'a a kan ƙara 135 a gaban Babbar Kotun Tarayya.
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama mutum 1,860 da ake zargi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi tare da ƙwace kilogiram 5,409.814 na miyagun ƙwayoyi a jihar Kano tsakanin watan Janairu zuwa watan Satumbar shekarar 2026.
Hukumar ta kuma yi nasarar ganin kotu ta hukunta mutum 89 sannan ta shigar da ƙara 126 a gaban kotuna a cikin watanni taran, yayin da ake ci gaba da shari'a a kan ƙara 135 a gaban Babbar Kotun Tarayya.
Runduna ta musamman ta NDLEA a Kano ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in watsa labaranta, Sadiq Muhamma Maigatari, ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce waɗanda ake zargin sun haɗa da mata 92, yayin da miyagun ƙwayoyin da aka ƙwacen sun haɗa da wiwi da hodar iblis da da ƙwayoyi masu sa maye da sauran miyagun ƙwayoyi.
Rundunar ta ce ta kuma aiwatar da matakai na ba da shawarwari da magani da gyara hali ga kimanin mutum 1,700 da shan miyagun ƙwayoyi ya shafa da kuma kimanin shirye-shirye na wayar da kan jama’a a 420 a makaranti da al’ummomi.
Ta ce aikin dawo da doka da oda na Operation Restore Order, wanda aka ƙaddamar a ƙarƙashin umarnin shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya.), ya janyo tarwatsa kimanin dabar ƙwaya 35 da aka gano da kuma kama kimanin waɗanda ake zargi fiye da 300.
Samamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile harkar rarraba miyagun ƙwayoyi da kuma inganta tsaron al’ummomi a faɗin jihar.
Rundunar ta kuma ba da rahoton gano wata hanya ta ƙarƙashin ƙasa a yankin Rimin Kebe na cikin garin Kano a ƙarƙshin aikin da aka yi wa laƙabi da Operation Sharar Mafaka
Sanarwar ta ce, masu dillancin miyagun ƙwayoyi suna amfani da wurare na ƙarƙashin ƙasa domin ɓoye da kuma aikata harkoki mara kyau, tana mai bayyana ƙalubalen da ma’aikata ke fuskanta wajen daƙile aika-aikar masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Kwamandan rundunar, CN DY Lawal, ya yaba wa Marwa bisa jagorancinsa da jajircewarsa kan aikin hukumar.
Lawal ya yi kira ga mazauna jihar su ba da bayanai masu tushe a kan lokaci ga hukumar, yana mai jaddada cewa sa hannun mutane gari da haɗin kansu na da muhimmanci wajen daƙile laifuka masu alaƙa da miyagun ƙwayoyi.

