Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino, ya bayyana wasan a matsayin “wani abin ban mamaki” duk da cewa an tashi canjaras da shi a gida.
Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta ba da mamaki yayin da ta rike Manchester City suka tashi da ci 4-4 a wasan Gasar Firimiya a karshen mako.
Haaland ne ya fara zura kwallo a ragar Chelsea ta hanyar bugun fenareti mai cike da ce-ce-ku-ce.
Sannan Thiago Silva ya rama wa Chelsea, yayin da Raheem Sterling ya ci tsohuwar kungiyarsa inda wasan ya koma 2-1.
Sai dai kuma Manuel Akanji dan asalin Nijeriya ya rama wa City abin da ya sa wasan ya koma 2-2.
Dawowa daga hutun rabin lokaci ke da wuya sai Haaland ya zura kwallo a ragar Chelsea.
Jackson ya rama wa Chelase a minti na 67 inda wasa ya koma 3-3
Haka aka yi ta fama tsakanin kungiyoyin biyu har minti 86 inda Rodri ya zura wa City kwallo ta hudu a ragar Chelsea.
A wannan lokacin kusan kowa ya yarda cewa City ta ci wasan, sai dai ‘yan Chelsea ba su karaya ba.
Kuma a minti na 95 Chealsea ta samu bugun fenareti inda Cole Palmer ya zura kwallo a ragar City .
"Gasar da ta fi ko wacce a duniya"
Tun da aka tashi wasan 4-4 ne dai mutane suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu game da wasan da aka fafata.
Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino, ya bayyana wasan a matsayin “wani abin mamaki” duk da cewa an tashi da ci 4-4 da kungiyarsa a gida.
"Abin mamaki ne – shi ya sa Gasar Firimiya ce gasar da ta fi rashin tabbas a duniya. Kowa na son ya kasance cikin wasan na ban mamaki," in ji shi.
"Abu mai wuya ne mutum ya yi magana domin kowa na son ya bayyana irin yadda wasan ya burge shi. Manchester City ce kugiyar da ta fi karfi a duniya, kuma Chelsea ta nuna jarumtaka inda ta yi kokarin samun maki uku,” a cewarsa.
Wasan dai shi ne wasan farko da aka rama ci sau hudu a Gasar Firimiya tun shekara 2009, kuma shi ne wasa na biyar a tarihin gasar gaba daya da aka samu irin wannan sakamakon.
"Wasan talla ne mai kyau da kuma nishadantarwa ga Gasar Firimiya," a cewar Guardiola. "Kungiyoyin biyu sun nemi yin nasara . Ba zan tsammani wani abu akasin haka ba. Chelsea na da ‘yan wasa masu ban mamaki."