Sport
Dollar
40,2184
0.11 %Euro
46,9873
-0.19 %Gram Gold
4.340,4000
0.12 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ankara na sanya idanu cikin tsanaki kan ‘yan ta’addan PKK da ke ajiye makamai ta hanyar Hukumar Leƙen Asiri da Rundunar Sojin Turkiyya, in ji Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa ana buɗe ƙofofin sabon shafi ga ƙasarsa kuma manufofin “Shekaru 100 na Turkiyya” na zama gaskiya.
“Sabon zamani na bullo wa a kasarmu. Daya bayan daya, muna cim-ma manufofinmu na Shekaru 100 na Turkiyya inda suke zama gaskiya,’ in ji Erdogan a ranar Lahadi a wajen Taron Tuntubar Juna da Tsinkaye na Jam’iyyar Adalci da Cigaba (AK) karo na 32 a Ankara.
Game da Ayyukan Samar da “Turkiyya Marar Ta’addanci”, shugaban ya ce “Muna ganin cewa sakonninmu, wadanda ke kara tabbatar wa ga abokai d a’yan uwanmu, inda suke kuka saka tsoro da fargaba a zukatan abokan hamayya da makiya, na isa ga inda ake so.”
Ya bayyana cewa Ankara na sanya idanu cikin tsanaki kan ‘yan ta’addar PKK da ke ajje makamai ta hanyar Hukumar Leken Asiri da Rundunar Sojin Turkiyya, in ji Recep Tayyip Erdogan.
“Muna sane da wadanda suke yakarmu. Ba abokanan adarmu ne karnukan ba, wadand asuke saka su aikin ne karnuka,” in ji Erdogan.
“Muna kan turbar kubutar da kasarmu baki daya daga ta’addanci da aka kakaba tun shekaru 47 da suka gabata,” in ji Erdogan, yana mai kara wa da cewar “Tuni muka fara ganin kwararan alamun tabbatar hakan.”
Ya kuma bayyana fatansa na cewa dukkan jam'iyyun siyasa tare da rukunonin 'yan majalisu za su goyi bayan matakin da za a dauka a majalisar dokokin Turkiyya, yana mai jaddada cewa babu wanda ke da hakkin kawo cikas, ko tauyewa, ko yin zagon kasa ga wannan tsari, musamman ma kada a yi amfani da lamarin don biyan wasu ‘yan bukatu na siyasa.
A rayuwa da siyasa, kusan za a iya biyan komai, amma babu wani abin da zai kawo cikas ga wannan lamari mai muhimmanci, wanda ya shafi hadin kai, goyon baya, zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umarmu su miliyan 86, in ji shi.
"Duk abin da za mu yi, muna yin shi ne da la'akari da dukkan al'ummarmu a zukatanmu, musamman 'yan uwan shahidanmu da kuma tsaffin sojojinmu, tare da yin la'akari da makomar kasarmu," in ji shugaba Erdogan.
Shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa, kada a manta cewar wannan sabon zamani, da ake tsara ma'auninsa, ya dora muhimman alhaki ba kawai ga jam'iyyar JAdalci da Cigaba (AK), Jam’iyyar ‘Yan Kishin Kasa (MHP), Dimokuradiyya da Daidaiton Al’uma ba, da dukkan bangarorin siyasa da ma ‘yan siyasar kansu.
Comments
No comments Yet
Comment