Dollar

40,1901

0.22 %

Euro

47,1146

0.08 %

Gram Gold

4.336,9600

1.24 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

“Yau sabuwar rana ce; an bude sabon shafi a tarihinmu,” in ji Erdogan a ranar Asabar, inda ya kira wannan matakin a matsayin wani muhimmin mataki na kawo ƙarshen abin da ya kira “masifa ta shekaru 47 ta ta'addanci.”

Turkiya ta yi nasara, in ji Erdogan bayan 'yan ta'addan PKK sun ajiye makamansu

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya sanar da wani babban sauyi a yaƙin da ƙasar ta shafe shekaru tana yi da ta'addanci, bayan ajiye makamai da 'yan ta'addan PKK suka yi a arewacin Iraki, wanda wannan wani muhimmin lamari ne a tarihi.

“Yau sabuwar rana ce; an bude sabon shafi a tarihinmu,” in ji Erdogan a ranar Asabar, inda ya kira wannan matakin a matsayin wani muhimmin mataki na kawo ƙarshen abin da ya kira “masifa ta shekaru 47 ta ta'addanci.”

A ranar Juma’a, wasu ‘yan ta’addan PKK guda 30 sun ƙona makaman su a bakin wani kogo a arewacin Iraƙi — wani mataki mai cike da tarihi da Ankara ta fassara a matsayin farkon rushewar ƙungiyar.

Wannan ci gaban ya zama ɗaya daga cikin manyan alamu a yaƙin da aka shafe shekaru ana yi tsakanin Turkiyya da PKK, wadda Ankara, Amurka, da EU suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

“Tun daga jiya, masifar ta'addanci ta fara shiga matakin ƙarewa,” in ji Erdogan. “Turkiyya ta fara rufe wani babi mai cike da ƙunci da zubar da hawaye. An buɗe ƙofofin wata babbar Turkiyya mai ƙarfi.”

Samar da Turkiyya maras ta’addanci

Yayin da yake bayyana wannan lokaci a matsayin warkar da ƙasa da kuma nasarar dabarun siyasa, Erdogan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa wajen ganin Turkiyya ta zama ba tare da ta'addanci ba, yana mai alkawarin ci gaba da haɗin kai da gyaran doka.

“Za mu kafa wani kwamiti a majalisar dokokinmu don tattauna buƙatun doka na wannan tsari,” kamar yadda ya sanar. “Za mu yi aiki tare, kafada da kafada, kuma za mu shawo kan duk wani cikas.”

Erdogan ya jaddada cewa wannan nasara ba ta gwamnati kaɗai ba ce, amma ta dukkan al’ummar Turkiyya.

“Turkiyya ta yi nasara, al’ummata ta yi nasara. Turawa, Kurdawa, Larabawa—dukkan ‘yan ƙasarmu miliyan 86 sun yi nasara,” kamar yadda ya ce.

“Duk abin da muke yi, muna yi ne don Turkiyya, don al’ummarmu, don ‘yancin kanmu, don makomarmu.”

Yayin da yake jaddada matsayinsa mai ƙarfi kan ‘yancin ƙasa, Erdogan ya bayyana cewa: “Ba za mu bari kowa ya take darajar ƙasarmu ba, kuma ba za mu taɓa sunkuyar da kawunanmu ba. Ba za mu shiga wani shiri da zai yi barazana ga haɗin kanmu, ƙasarmu, al’ummarmu, ko zaman lafiyarmu ba.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#