Sport
Dollar
40,1726
0.22 %Euro
47,0769
0.06 %Gram Gold
4.336,0800
1.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Da yake bayar da misalin kamanceceniya tsakin kisan kiyashin Bosnia a 1995 da rikicin Gaza a yau, Erdogan ya zargi kasashen duniya da maimaita nuna halin ko in kula.
Turkiyya ta yi watsi da duk wasu kalamai da ra’ayoyi da ke neman musanta kisan kiyashin da aka yi a Srebrenica ko kuma "girmama masu aikata laifukan yaki" wanda hakan ya sabawa hukuncin kotun duniya, in ji shugaban kasar.
Kalaman na Recep Tayyip Erdogan sun zo ne a cikin wani sakon bidiyo na tunawa da cika shekaru 30 na kisan kiyashin da aka yi a Srebrenica a shekarar 1995, wanda ya kashe rayukan dubban 'yan kasar Bosniya.
Erdogan ya kuma nanata ci gaba da goyon bayan Ankara ba tare da wani sharadi ba ga 'yancin kan Bosnia da Herzegovina, 'yancin iyakoki, da aiki da kundin tsarin mulki.
Da yake tabo batun hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaza, Erdogan ya ce shekaru da dama da suka gabata, kasashen duniya sun yi gum da bakinsu kan Srebrenica, kuma a cikin 'yan shekarun nan, sun zuba idanu suna kallon zaluncin da ake yi a Falasdinu.
Erdogan ya sha alwashin cewa "ko ba dade ko ba jima" za a tuhumi gwamnatin Isra'ila a gaban kotu da tarihi kan kisan kiyashin da ta yi wa Falasdinawa kusan 58,000.
Comments
No comments Yet
Comment