Kungiyar Manchester City ta fitar da rahotonta na shekara-shekara na 2022/2023 wanda ya nuna gagarumar ribar da ta samu cikin shekaru biyu.

Manchester City ta samu kudin shigar da ya kai £712.8m a shekarar 2022/23

Manchester City ta fitar da rahoton kudaden shigar da ta samu a shekarar 2022/2023 wanda ya kai fam miliyan 712.8.

Hakan ya nuna cewa kungiyar ta samu karin £99.8m a kan kudin shigar da ta samu a bara sannan ya zarta £648.4m da kishiyarta Manchester United ta samu a shekarar kudi ta 2022/2023 .

Kazalika City ta samu ribar £80.4m , wato kari kan £41.7m da ta samu a bara.

Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ce a shekarar da ta lashe kofuna uku, wato Kufun Gasar Firmiya da na FA da kuma na Zakarun Turai, inda ta kasance ta biyu da ta dauki kofuna uku a kakar wasa daya bayan Manchester United wadda ta yi irin wanna bajinta a 1999.

Rahoton ya nuna muhimman hanyoyin uku da ke samar wa kungiyar kudaden shiga da suka hada da kasuwancinta da watsa shirye-shirye da kuma tsare-tsarenta na gudanarwa.

#