Dollar

39,0327

0.29 %

Euro

44,1939

0.3 %

Gram Gold

4.144,4000

0.51 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Majalisar Wakilan Nijeriya a ranar Litinin ta bayar da umarnin da a bayar da tsaro na tsawon shekaru 10 ga ɗan jarida mai bincike Umar Audu, da bincikensa ya bankaɗo yadda ake sayar da digirin bogi a Jami’o’in Jumhuriyar Benin ga ‘yan Nijeriya.

Majalisar Nijeriya ta amince a bai wa ɗan jaridar da ya bankaɗo digirin bogi kariyar shekara 10

Majalisar Wakilan Nijeriya a ranar Litinin ta bayar da umarnin da a bayar da tsaro na tsawon shekaru 10 ga ɗan jarida mai bincike Umar Audu, da bincikensa ya bankaɗo yadda ake sayar da digirin bogi a Jami’o’in Jumhuriyar Benin ga ‘yan Nijeriya. https://www.trt.global/afrika-hausa/article/d6e1b7a0f472

Kwamitin Hadin Gwiwa na Jami’o’i, Kwalejojin Fasaha da Ma’aikatun Harkokin Cikin Gida da Harkokin Waje, da Cigaban Matasa, wanda a yanzu ke binciken abun kunyar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito.

Idan za a tuna, a wani binciken karkashin kasa da Audu ya gudanar, ya bankado yadda ‘yan Nijeriya ke zuwa kasar Benin da sunan karatu inda suke sayen takardun kammala matakan digiri daban-daban, wanda wasun su ma hukumomin Nijeriya sun amince da su, ciki har da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Ɗan jaridar ya bayyana yadda wadanda suka sayo takardun kammala karatun suke gogayya da wadanda suka sha wahala suka yi karatu a jami’o’in gida da na waje.

Haka zalika ya bayyana cewa, irin fannin karatu da matakin digiri ne ke bayyana kudaden da za a biya don sayen takardun kammala jami’ar.

Ɗan jaridar ya gana da wani ejan, kuma ya sayi takardar kammala Jami’ar Ecole Supérieure de Gestion et de Technologies, ESGT, Cotonou Jumhuriyar Benin a ranar 17 ga Fabrairu, 17.

Ya samu karbar takardun ne bayan ɗan jaridar ya biya wani adadi na kudi, ciki har da kudin makaranta na wa’adin irin karatunsa.

Da yake jawabi game da batun, shugaban kwamitin, Abubakar Fulata, ya sanar da cewa sun bukaci hukumar ‘yan sandan Nijeriya da Hukumar Tsaron Farar Hula ta Nijeriya da su tabbatar da tsaron Audu.

“Mun yaba wa Audu saboda gwarzantakar da ya nuna. Mun bukaci Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da tabbatar da Hukumar Tsaron Farar Hula ta samar da tsaro tare da ‘yan sanda gare shi,” in ji Fulata.

A lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin, Audu ya kuma bayyana yadda ya samo tkardun digiri a jami’ar Jumhuriyar Benin ba tare da zuwa aji ba, sanna daga baya Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya a Nijeriya ta amince da tkardun bayan biyan Naira 40,000.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#