United ta biya kungiyar Ajax fam miliyan 86.3 kan Antony inda ya zama dan wasanta na biyu mafi tsada, sai dai kawo yanzu dan wasan na Brazil bai taɓuka wani abin a zo a gani ba tun da ya dawo wajen Kocin Manchester United Erik Ten Hag ba.
Har yanzu dan wasan Machester United Antony ya kasa zura ƙwallo ko ɗaya a raga a kakar wasa ta bana, duk da kasancewarsa ɗan wasan na biyu mafi tsada da aka saya a bara.
"An shafe wasu 'yan makonni ba ya nan, kuma hakan ya kawo masa cikas a ci gabansa. Ko da yake yana da kyakkyawar makoma a gaba, hutun da ya samu zai yi matuƙar tasiri wajen ƙara masa ƙwazo tare da dawo masa da matsayinsa.
"Wannan tsari ne mai ƙalubale," a cewar Kocin Machester Uniter Erik ten Hag, yayin jawabinsa ga manema labarai.
Sai dai Erik Ten Hag ya ce yana da yaƙinin cewa "ce-ce-ku-cen" da ake yi a kan Antony ce ta shafi ƙwazonsa a kulob ɗin.
A wasanni 10 da ya buga a kakar wasa ta bana, ɗan wasan mai shekara 23 ya kasa zura ƙwallo ko taimakawa a wasanni, kuma lokacin da aka dawo da Antony United a gasar wasan cin Kofin Champions League na ƙungiyar da Newcastle inda ya ba da gudunmawar da ta kai ga ci 3 -0.
United ta biya ƙungiyar Ajax fam miliyan 86.3 kan Antony inda ya zama ɗan wasanta na biyu mafi tsada, sai dai kawo yanzu ɗan wasan na Brazil bai taɓuka wani abin a zo a gani ba tun da ya dawo wajen Ten Hag a United ba.
Antony bai samu damar buga wasanni biyar a farkon wannan kakar ba, sakamakon hutun da ya dauka don ya halartar gayyatar 'yan sanda a watan Satumba kan batun zargin cin zarafin da wata tsohuwar budurwarsa ta yi masa.
Da aka tambayi Kocin ko Antony ''ya dace da irin zaton da suka yi a kansa a lokacin da aka sanya hannu wajen sayensa'', Ten Hag ya ba da amsar cewa, "Koƙarin hadin gwiwa ce, musamman daga kungiyar.
"Ƴan wasan ba za su iya wata rawar gani ba idan har ba a ba su ƙwallo ba, kuma ni ma ina da alhaki kan hakan," in ji shi.
"Amma a zahiri, ana ce-ce-ku-ce sosai a kansa, kuma hakan ya yi tasiri wajen rage masa karsashi. Zai iya rawar gani, kazalika sauran 'yan wasan ma za su iya rawar gani.
"Shi ma Antony jarumi ne, yana da ƙwazo sannan jajirtacce ne, ina da yaƙinin zai kawo mana wasan da ya dace da mu," in ji Erik ten Hag.