Al'ummar Turkiyya na adawa da tsarin amfani da katin biyan kudi na Visa da Mastercard kan goyon bayan da suke bai wa Isra'ila, wanda hakan ya sanya TROY ya maye gurbinsu a matsayin wanda aka fi so.

Katin cire kudi na TROY na Turkiyya ya samu karbuwa yayin da ake kaurace wa Isra'ila

Wani yunƙuri na nuna goyon baya ga al'ummar Gaza na ci gaba da samun karɓuwa a Turkiyya, a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a yankin Gaza na Falasdinu tsawon wata guda, tare da kashe aƙalla Falasdinawa 10,500.

Daidaikun mutane da kamfanoni da kungiyoyin al'umma da masu zaman kansu sun kasance suna juyawa kayayyakin Isra'ila baya suna maye gurbinsu da wasu, don nuna adawa da yaƙin da Isra'ilan ke yi da Gaza.

"Bayan kisan kiyashin da Isra'ila take yi wa Falasdinawa a Gaza, ya zama wani al'amari muhimmi a yanke hulɗa da hanyoyin da ke samar da kudade ga kasar," in ji wata mai zane a Istanbul Feride Karatas, wadda ta shiga sahun ƙaurace wa Isra'ila a hirarsa da TRT World.

"Ina da 'ya'ya biyu; Ba zan iya kallon yara a Falasdinu suna shan wahala, suna cikin tsoro da rawar jiki da kuka ba tare da taimako ba, su kaɗai. ... Shi ya sa ni da ƙawayen da ke kusa da ni muke ƙoƙarin yin duk abin da za mu iya,” in ji ta

Ba tare da wata tangarda ba, miliyoyin al'ummar Turkiyya ma sun fara ƙauracewa tsarin amfani da katunan Visa da Mastercard - domin rage kamashon da kamfanonin ke samu daga hada-hadar katunan.

A gefe guda kuma, mutane a faɗin Turkiyya sun ƙara nuna sha'awarsu ga amfani da TROY wanda Turkiyya ta samar, wanda ke nufin "Türkiye's Payment Method” wato "Hanyar Biyan Kuɗi ta Turkiyya" Karatas na ɗaya daga cikin waɗannan mutanen.

Da samun labarin TROY, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen sauyawa zuwa amfani da shi, tare da kwaɗaitar da jama'arta yin hakan.

"Haƙiƙa ƙauracewa kayayyakin mutum ɗaya yana da muhimmanci. Amma babban tushen samun kudin kasar nan shi ne katin Mastercard da Visa da muke amfani da su kusan kowace rana," in ji ta.

Karatas ta ƙara da cewa, wani kamasho na tafiya ne ga kamfanonin da ke tallafa wa Isra'ila daga kowane amfani da aka yi da katin Mastercard da Visa, ko da kuwa 'yan kasar za su ci dinga amfani da su ne kawai ta wajen sayen kayayyakin cikin gida, Karatas ta ƙara da cewa: "Babbar ƙauracewa ita ce yanke wannan hanyar samun kudin shiga."

#