Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 246 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,731— kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 83,530 sun jikkata, a cewar jami'ai.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe mutum 11 da jikkata da dama a wani sabon hari da ta kai Gaza

1033 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 11 da jikkata da dama a wani sabon hari da ta kai Gaza

Akalla Falasdinawa 11 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza.

Kamfanin dillancin labaran na WAFA ya ruwaito akwai wasu gommai da suka jikkata sakamakon wannan harin na safiya.

Rahotannin sun bayyana cewa jami’an kare farar hula sun yi ƙoƙarin gano gawawwaki biyar daga ciki har da na yara da mata daga cikin ɓaraguzai, bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari a gidan iyalan Mhanna da ke unguwar Sheikh Radwan.

Sannan kuma hare-haren na Isra’ila sun kai hari wani gida da ke sansanin gudun hijira na Al Bureij wanda ke a tsakiyar Gaza inda mutum shida suka rasu da jikkata da dama.

1010 GMT — Masu zanga-zanga na shirin yi wa Fadar White House 'ƙawanya' kan rikicin Gaza

Magoya bayan Falasɗinu da ke fafutikar ganin an kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma goyon bayan da Amurka ke bayarwa, na shirin yin ƙawanya ga Fadar White House ta Amurka a ƙarshen makon nan.

Ƙungiyoyin gwagwarmaya irin su CODEPINK da Council on American Islamic Relations a ranar Juma’a sun bayyana cewa an shirya yin zanga-zanga a ranar Asabar, a lokacin da za a cika wata takwas ana yaƙin Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma jefa mutane cikin bala’i da yunwa.

Amurka wadda babbar ƙawar Isra’ila ce, an ta yi mata bore iri-iri a Washington da kuma wurare da ke kusa da White House, zuwa rufe hanyoyi kusa da tashoshin jirgin ƙasa da kwalejoji.

Akalla jami'ai takwas ne suka yi murabus daga gwamnatin shugaba Joe Biden, saboda rashin amincewarsu da manufofinsa. Masu zanga-zangar sun kuma dakile wasu lamuran yakin neman zaben Biden.

#