Kungiyar Hadin Kan Kasashen Gulf ta yi maraba da wani kuduri da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar, wanda ke bukatar mayakan Houthi su dakatar da hare-harensu nan take.

Kasashen Gulf sun yi maraba da matakin MDD na kira ga mayakan Houthi su dakatar da hare-hare

Sakatare-Janar na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa na Tekun Fasha (GCC), Jassem Mohamed Albudaiwi, ya yi maraba da wani kuduri da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar, wanda ke bukatar mayakan Houthi su dakatar da hare-harensu nan take.

Albudaiwi ya bayyana cewa ya yi maraba da hadin kan Ƙasashen duniya kan kudurin Kwamitin Sulhu Tsaro Majalisar Dinkin Ɗuniya mai lamba 2837, wanda ke buƙatar mayakan Houthi, waɗanda aka ayyana a matsayin 'yanta'adda, su dakatar da tsananta ayyukan soji da hare-harensu nan take ba tare da wani sharadi ba, ciki har da hare-haren da ke shafar fararen-hula da muhimman ababen more rayuwa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Jumma'a.

Sakatare-Janar din ya kuma yaba da ƙoƙarin Birtaniya wajen gabatar da daftarin kudurin.

A cewarsa, kudurin wani babban mataki ne na karfafa matsayar ƙasashen duniya ta kin amincewa da hare-haren mayakan Houthi.

GCC ta sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Yemen da duniya ta amince da ita

Albudaiwi ya kuma yi kira da a mayar da kudurin zuwa wani tsayayyen alkawari na dakatar da hare-haren mayakan Houthi.

Ya sake jaddada goyon bayan kungiyar GCC ga gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita, domin kiyaye ikon kasar, hadin kan al'ummarta da kuma zaman lafiyarta.

Yemen na cikin rikici tun shekarar 2014, lokacin da mayakan Houthi suka ƙwace ikon babban birnin kasar, Sanaa, da wasu larduna.

Lamarin ya sa kawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta shiga yakin a shekarar 2015, domin taimaka wa gwamnatin kasar.

An samu wani dan lokaci na kwanciyar hankali tun daga watan Afrilun 2022, amma sabon fadan da ya barke a watan Yuli ya kawo karshen wannan yanayi, inda mutane 12,000 suka mutu ko suka jikkata, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: AFP (Wire)

#