Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 411 a yau — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 43,972 tare da jikkata fiye da mutum 104,008. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,544 tun daga watan Oktoban 2023.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari da bama-bamai a Gaza, Falasɗinawa 20 sun mutu ko sun ɓata

Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024

2300 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden bama-bamai a gidan wani mutum mai suna Joudeh da ke Tsohon Titin Gaza a yankin Jabalia al-Balad na arewacin Gaza, inda Falasɗinawa 20 suka mutu ko kuma suka ɓata, a cewar wasu ganau da kuma wasu rahotanni daga yankin.

Kafofin watsa labaran yankin sun ce mutum 12 sun mutu sakamakon luguden wutar da jiragen yaƙin Isra'ila suka yi.

Cibiyar samar da bayanai kan Falasɗinawa ta Palestinian Information Center, ta ce mutum 10 sun ɓata.

A gefe guda, an jikkata wani ɗan jaridar Gaza Hossam Shabat wanda ke jerin manema labarai da Isra'ila take so ta kashe, kamar yadda Shabat ya wallafa a shafinsa na X.

"A daren nan, dakarun Isra'ila sun kawo mini hari da gangan. Bayan na samu labarin tashin bam a maƙotanmu, na tsere cikin motata domin bayar da rahoto. Lokacin da na isa gidan da lamarin ya faru, na ga mutane a kiɗime suna ihu domin neman agaji daga hawa na biyu na ginin," in ji shi.

"Lokacin da na shiga gidan, an sake kai masa hari inda wasu sassani jikin mutane suka faɗo kaina. Ɓuraguzai sun faɗo a kaina da kuma kan abokan aikina. An kashe ɗaya daga cikin mutanen da suka soma isa gidan yayin ni da wani abokin aikina muka jikkata, kuma wasu da dama sun riga mu gidan gaskiya."

#