Murat Kurum na Turkiyya ya buƙaci taron COP31 ya aiwatar tare da cika alƙawura da aka ɗauka, ta hanyar mayar da su ayyukan da za a iya gani, tare da ƙarfafa tattaunawa da kuma tallafa wa ƙasashen da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi.

Kurum ya buƙaci taron COP31 ya mayar da alƙawuran yaƙi da sauyin yanayi zuwa ayyuka na zahiri

Turkiyya ce ke karbar baƙuncin taron COP31, ƙarƙashin shugabancin Ministan Muhalli da Birane da kuma Sauyin Yanayi na ƙasar, Murat Kurum, yayin da Ministan Sauyin Yanayi da Makamashi na Australia, Chris Bowen, ke jagorantar tattaunawar taron.

Da yake jawabi a zaman bude taron, Kurum ya yi gargadin cewa rikice-rikicen siyasar kasa da kasa da rashin tabbas a tattalin arziki da kuma karuwar illolin sauyin yanayi, kalubale ne masu alaka da juna.

“A yanzu, manufofin sauyin yanayi su ne manufofin ci gaba. Su ne manufofin samar da abinci, da makamashi, da birane da kuma kiwon lafiya,” in ji shi.

Kurum ya bayyana cewa Turkiyya na son ganin COP31 ya zama taron aiwatar da alkawura, bisa tattaunawa, da cim ma matsaya daya da kuma daukar matakai na zahiri.

“Wannan shi ne sakon Antalya: A kara fadada tattaunawa yayin da ake samun rarrabuwar kawuna. A dawo da aminci a inda aka samu tangarda. A tabbatar an yi amfani da albarkatu yadda ya kamata yayin da bukatu ke karuwa. A rage gibin da ke tsakanin alkawuran da muka dauka da kuma rayuwar al'umma,” in ji Kurum.

Ya kuma gabatar da wani shiri mai suna 'Alkawarin Samar da Wutar Lantarki ta Duniya na 35 zuwa 2035', wanda ke da nufin kara kaso na amfanida wutar lantarki zuwa kashi 35 cikin 100 na makamashin da ake amfani da shi a duniya nan da shekarar 2035.

Haka kuma, ya bukaci kasashe su cika alkawuran tallafin kudaden yaki da sauyin yanayi, ciki har da samar da akalla dala biliyan 300 a duk shekara ga kasashe masu tasowa nan da shekarar 2035.

A ranar Litinin ne dai aka bude taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP31 a birnin Antalya na kasar Turkiyya, inda shugabanni suka yi kira da a gaggauta daukar matakan aiwatar da alkawuran da suka shafi sauyin yanayi, da makamashi mai tsafta da kuma hada tallafin kudi ga kasashen da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi.

Taron, wanda zai gudana daga ranar 9 zuwa 20 ga watan Nuwamba, ya hada wakilai daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna hanyoyin rage hayakin da ke dumama yanayi, da daukar matakan sauyin yanayi da kuma samar da kudaden tallafi.

Mayar da hankali kan kudaden tallafi da sauya fasalin makamashi

Chris Bowen ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa, yana mai gargadin cewa dumamar yanayi za ta wuce matakin digiri 1.5 na ma'aunin Celsius da yarjejeniyar Paris ta shimfida idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

“Sabbin bayanan kimiyya sun nuna cewa za mu wuce matakin digiri 1.5. Amma akwai yiwuwar za mu iya komawa karkashin wannan mataki idan muka yi aiki tare cikin gaggawa, da kuma hadin kai da azama,” in ji shi.

Ya bayyana cewa jarin da aka zuba a makamashi mai tsafta a duniya ya kai kusan dala tiriliyan 2.2 a bara, wanda ya kusan ninka jarin da aka zuba a makamashin man da aka samu daga kasa.

Sai dai ya yi gargadin cewa har yanzu kasashe masu tasowa na fuskantar matsaloli wajen samun kudaden tallafi na yaki da sauyin yanayi.

“Kasashen da suka fi bukatar tallafin kudaden sauyin yanayi su ne suka fi karancin samu,” a cewar Bowen yana mai kira da kudaden cikin sauri da adalci.

Ya kuma sanar da wani shiri wanda za su gabatar tare da Kurum, domin samar da wata matsaya ta musamman da za ta mayar da hankali kan hanzarta aiwatar da hanyoyin magance sauyin yanayi a aikace, ba tare da sake maimaita tattaunawar da ake gudanarwa a wasu matakai ba.

Shugaban MDD kan sauyin yanayi ya bukaci mafita ta zahiri

Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da sauyin yanayi, Simon Stiell, ya bukaci taron COP31 da ya dora daga batun tsara manufofi da alkawura zuwa ga kwararan matakai na zahiri da za su fadada amfani da makamashi mai sabuntawa da kuma karfafa hanyoyin rarraba watar lantarki da rage hayakin Methane.

“idan muka hada kai da daukar matakan rage hayakin methane da kuma fadada amfani da wutar lantarki za mu iya taimakawa wajen rage hasashen dumamar yanayi da rabin digiri na ma'aunin Celsius,” a cewar Stiell.

Haka kuma, ya bukaci kasashe su kara kudaden tallafin shirye-shiryen aiwatar da matakai tare da cika alkawuran da suka dauka a baya, yana mai jaddada cewa dole ne a bai wa kasashen da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi muhimmanci a yayin batun sauya fasalin makamashi.

TRT Afrika — TRT Afrika

#