Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 268 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,834  — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 86,858 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500.

Kai-tsaye: Ba ci gaba a tattunawar sulhu, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza

0650 GMT — Ba ci gaba a tattunawar sulhu, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza

Harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai da sanyin safiyar Lahadi sun kashe Falasdinawa bakwai tare da jikkata wasu da dama a Gaza.

Hare-haren sun faɗa kan gidaje a Rafah da birnin Gaza, inda aka samu asarar rayukan fararen hula da suka haɗa da kananan yara kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito.

Haka kuma makaman atilari sun yi luguden wuta a kudancin Rafah da tsakiyar Gaza, da kuma a birane da ke gabashin Khan Yunis. A unguwar Daraj da ke Gaza, farar hula ɗaya ya rasu da dama kuma sun jikkata a wani hari da sojojin na Isra’ila suka kai wani gida.

0036 GMT — Masu shiga tsakani daga Amurka, Turai da ƙasashen Larabawa sun ƙara ƙaimi wajen ganin an kauce wa shiga gagarumin yaƙi tsakanin Isra'ila da mayaƙan Hezbollah na ƙasar Lebanon waɗanda ke samun goyon bayan Iran, suna masu fargabar watsuwarsa zuwa sauran sassan Gabas ta Tsakiya kamar yadda aka yi hasashe watanni da dama da suka wuce.

Iran da Isra'ila sun yi musayar yawu ranar Asabar sannan Iran ta ce yaƙin da za a yi zai kasance "mai matuƙar muni".

Yanzu dai babu tabbas game da tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda hakan ne kawai zai sa Hezbollah da sauran ƙungiyoyi da Iran take mara wa baya su sauƙaƙa shirinsu na gwabza yaƙi da Isra'ila.

Ganin cewa babu ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta, jami'an diflomasiyya na Amurka da sauran ƙawayenta sun gargaɗi Hezbollah game da far wa Isra'ila da yaƙi.

#