Sport
Dollar
41,0483
0 %Euro
47,8442
0.02 %Gram Gold
4.474,1900
-0.09 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya ba ta ce komai a kan lamarin ba, sannan ba a san musabbabin faruwar hatsarin ba.
Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata.
Lamarin ya faru ne a garin Asham, kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook, Imo Onyekwere ya fara wallafa faruwar lamarin kai-tsaye ta bidiyo a shafinsa.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna.
A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda taragun jirgin suka tuntsura, kuma mutane sun taru a wajen suna kallon abin da ya faru da ƙoƙarin aikin ceto, yayin da wasu da suka fi kama da fasinjoji na tsaye cirko-cirko.
Hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya, NRC ta ce tuni an tura tawagogin agaji da na jami'an lafiya don kai waɗanda suka jikkata asibiti.
Comments
No comments Yet
Comment