Sport
Dollar
41,0455
-0.02 %Euro
47,8488
0 %Gram Gold
4.473,4400
0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya gabatar da mutanen da aka ceto ɗin ga manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.
Gwamnatin Nijeriya ta yi nasarar kubutar da mutum 128 daga hannun ‘yan bindiga a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.
Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya gabatar da mutanen da aka ceto ɗin ga manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.
A cewar Ribadu, aikin ceton ya nuna sabbin dabarun tsaron kasa da kuma irin namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi.
Ya ce za a kula da lafiyar mutanen da aka ceto da kuma ba su tallafi don komawa cikin iyalansu da al'ummominsu.
Ribadu ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar sojoji, ‘yan sanda, jami’an leken asiri, da sauran hukumomin da suka yi aikin ceton.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace domin yaƙar ‘yan fashi da ta’addanci.
Comments
No comments Yet
Comment