Rahoton ya nuna cewa ɗurƙushewar siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewa suna barazana ga zaman lafiyar Isra'ila yayin da take tunkarar zaɓen watan Oktoba.
Wani rahoton binciken sirri na Amurka ya yi gargaɗin cewa taɓarɓarewar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa a cikin gida a Isra’ila suna iya jefa ta cikin yaƙin basasa ko rushewar gwamnati.
Rahoton, wanda aka yi wa take da "Durƙushewa Daga Cikin Gida", kana aka tattaro shi a watan Agusta ƙarƙashin Sashen Red Cell na CIA - wani sashe na musamman da aka bai wa alhakin ƙalubalantar yarjejeniyar leƙen asiri da kuma samar da wasu dabaru - kamar yadda wata kafar bincike mai zaman kanta ta Drop Site News ta ruwaito, tana ambaton majiyoyi biyu na Amurka da suke da masaniya kan batutuwan.
Rahoton ya nuna cewa Isra’ila na fuskantar matsin lamba mai tarin yawa a cikin gida, wanda ke zuwa a daidai lokacin da ƙasar ke shirin gudanar da zaɓen majalisar dokoki a ranar 27 ga watan Oktoba.
Manyan matsalolin sun haɗa da tsananin matsin tattalin arziki da yawan kashe kudaɗe kan harkokin tsaro da ƙaruwar tashin hankali na 'yan gudun hijira a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, da kuma tsananin fushin al'umma kan ƙin tilasta wa Yahudawa masu tsattsauran ra'ayin addini yin aikin soja.
Rashin jinƙai, durƙushewar siyasa da tsananin damuwa
Rahoton ya ce nacewar da Firaministan Benjamin Netanyahu ya yi na ci gaba da zama a kan mulki shi ne babban abin da ke haddasa rashin zaman lafiya a tsarin mulki da siyasar Isra’ila.
Shekarun da Isra’ila ta kwashe tana yin kisan ƙare-dangi a Gaza da ci gaba da yaƙe-yaƙe a faɗin Lebanon da Iran sun ta'azzara rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar ƙasar, inda jami’an soji da yawa da suka dawo gida suka faɗa tsananin yanayin damuwa sakamakon tsawon lokacin da suka kwashe a fagen daga.
Kazalika tsarin aikin soja ya shiga ruɗani a cikin ƙasar, inda mutane da dama suke fushi saboda yadda ake tilasta musu yin aikin soja, yayin da a gefe guda aka yafe wa rukunin Yahudawa masu tsattsauran ra'ayin addini.
Rahoton na CIA ya jaddada waɗannan hujojji na cikin gida, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da ƙara keɓe diflomasiyya ta ƙasashen duniya - wanda ke nuna raguwar tallafin Amurka - na barazanar wargaza zaman lafiya na cikin gida a Isra’ila.

