An fara kama Uchechi Sunday tare da ’yarta mai shekaru 32 a bara, inda aka same su da miyagun ƙwayoyi daban-daban, ciki har da methamphetamine, tramadol, ganyen tabar wiwi da kuma tabar wiwi.

Hukumar NDLEA ta sake kama wata tsohuwa mai shekara 83 kan zargin safarar miyagun kwayoyi

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta sake kama wata tsohuwa mai shekaru 83 bisa zargin mallakar miyagun ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba, shekara guda bayan an same ta da laifin aikata irin wannan laifi.

NDLEA ta ce ta kama tsohuwar ne a ranar 7 ga Oktoba, tare da ƙwayar methamphetamine da tabar wiwi wadda aka samar a ɗakin gwaji da ta ɗaure a ƙugunta.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce a cikin wata sanarwa: “Yayin da yawancin kakanni masu shekaru 83 ke neman hutu, ba haka lamarin yake ba ga Mrs Uloma Uchechi Sunday, wadda aka sake kamawa, ƙasa da shekara guda bayan kama ta da gurfanar da ita a gaban kotu da kuma yanke mata hukunci kan irin wannan laifi.”

An kama Uchechi Sunday ne a wani ƙauye da ke Jihar Abia, a yankin kudu maso gabashin Nijeriya, bayan samun bayanan sirri. An same ta da giram biyu na tabar wiwi da kuma giram bakwai na methamphetamine.

Ana kallon Nijeriya a matsayin wata cibiyar safara da samar da miyagun ƙwayoyi da ake kai wa wasu ƙasashe, amma masu bincike da ma’aikatan kiwon lafiya sun ce wasu daga cikin ƙwayoyin suna shiga kasuwannin cikin gida.

Wani rahoto na Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) na shekarar 2024 ya nuna cewa ana kuma jigilar hodar heroin da methamphetamine daga Asiya ta yankin Afirka ta Yamma, a kan hanyoyin da suka taso daga gabashi da kudancin Afirka zuwa Turai.

An fara kama Uchechi Sunday tare da ’yarta mai shekaru 32 a bara, inda aka same su da miyagun ƙwayoyi daban-daban, ciki har da methamphetamine, tramadol, ganyen tabar wiwi da kuma tabar wiwi.

Ta amsa laifinta, inda aka yanke mata hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari ko kuma biyan tarar naira 200,000, kwatankwacin dala 150. Ta biya tarar, aka sake ta.

 

#