An dakatar da shi na ɗan wani lokaci bayan ɗan wasan mai shekaru 41, ya fice daga sansanin tawagar ƙasar Portugal da ke birnin Copenhagen, gabanin wasan ƙungiyar da Denmark a gasar UEFA Nations League.

Hukumar ƙwallon ƙafar Portugal ta dakatar da Ronaldo daga buga wa ƙungiyar ƙasar wasa

An dakatar da Cristiano Ronaldo na ɗan lokaci daga buga wa tawagar ƙasar Portugal wasa a ranar Asabar, bayan da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Portugal (FPF) ta buɗe binciken ladabtarwa a kan ɗan wasan mai shekaru 41, kan ficewarsa daga sansanin tawagar ƙasar.

Hukumar FPF ta ce sashen da ke kula da harkokin da ba na ƙwararru ba ya yanke shawarar fara binciken ladabtarwa a ranar 9 ga Oktoba, domin gano dalilin da ya kai ga Ronaldo ga barin sansanin tawagar.

Har yanzu ba a sanar da hukuncin ƙarshe ba. Hukumar ta bayyana cewa za a ci gaba da ɓoye bayanan binciken har sai an kammala shi.

Ronaldo ya bar sansanin tawagar Portugal da ke birnin Copenhagen, gabanin wasan ƙungiyar da Denmark a gasar UEFA Nations League, sakamakon saɓani da babban koci Jorge Jesus kan lokacin da yake ba shi na buga wasa.

A cewar Ronaldo, Jesus ya amince cewa ba zai buga wasannin Portugal da Norway da Denmark ba, a matsayin wani ɓangare na shirin kula da lafiyarsa da ƙarfinsa. Sai dai Ronaldo ya ce daga baya kocin ya sanar da shi cewa zai buga mintuna 30 a wasan da za su yi da Norway.

“Na ci gaba da motsa jikina tun daga hutun rabin lokaci, ina kallon mintuna suna tafiya, amma ba a kira ni ba. Kocin ya karya alƙawarin da ya yi mini,” kamar yadda Ronaldo ya bayyayana a wata sanarwa.

Portugal ta samu nasara a dukkan wasanni uku da ta buga a lokacin hutun wasannin ƙasashe, yayin da Gonçalo Ramos, wanda ya maye gurbin Ronaldo, ya zura ƙwallaye uku.

Daga baya, Ronaldo ya nemi afuwar abokan wasansa da magoya baya kan barin sansanin, inda ya ce a shirye yake ya amince da duk wani hukunci da hukumar za ta ɗauka a kansa.

Ronaldo ya ce: “Na amince cewa bai kamata na bar sansanin tawagar ƙasar ba.” Sai dai ya kuma soki kocin kan abubuwan da suka faru waɗanda suka kai ga ficewarsa.

Yanzu an miƙa shari’ar ga Hukumar Bincike da Ladabtarwa ta Hukumar Kwallon Ƙafa ta Portugal, amma har yanzu hukumar ba ta sanar da hukuncin ƙarshe ba.

 

#