Yarjejeniyar tsagaita wutar ta sa an saki Falasdinawa mata da matasa 39 daga gidajen yarin Isra'ila yayin da ita kuma Hamas ta saki Isra'ilawa 13 daga cikin wadanda ta yi garkuwa da su.
Falasdinawa a fadin Gabar Yammacin Kogin Jordan sun yi ta sowa da daga tutocin Falasdinu da na Hamas da kuma maratayin kaffiyeh bayan Isra'ila ta saki Falasdinawa 39 da take tsare da su shekara da shekaru.
"Ina cike da farin cikin amma 'yancina ya samu ne bayan mutane da dama sun yi shahada," in ji Marah Bakir, mai shekara 24, inda take magana a kan kusan mutum 15,000 da Isra'ila ta kashe a Gaza tun lokacin da ta kaddamar da hare-hare.
Hanan al Barghouti, mai shekara 58, wadda aka saka daga kurkukun Isra'ila bayan ta kwashe wata biyu, ta jinjina wa Hamas da shugabanninta da al'ummar Gaza.
Ta yi addu'ar "Allah ya saka musu da alheri. Idan ba domin al'ummar Gaza suke aiki ba da ba za mu samu 'yanci ba. "Muna cikin kurkuku muna shan ukuba. Matsiyata ne. Sun ci zarafinmu, sun wulakanta mu. Amma hakan bai sa mun sarayar da mutuncinmu ba, kuma muna godiya bisa wannan jajircewa da aka yi."
Ga hotunan wasu daga cikin mata da matasa da aka saka daga gidajen yarin Isra'ila.
Wani dattijo yana cike da murna lokacin da ya gana da Bafalasdiniya Fatima Amarneh a kusa da garin Jenin a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye./Hoto: Reuters
Falasdinawa fursunoni sun bar ofishin sojojin Isra'ila da ke Ramallah a Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye./Hoto:Reuters
Wasu daga cikin Falasdinawa da aka saka (sanye da riguna ruwan toka) suna shewa bayan sun fita daga kurkukun Ofer na sojin Isra'ila da ke Baytunia kusa da Gabar Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye./Hoto:AFP
Wata Bafalasdiniyi da aka saka daga gidan yari ta nuna alamar nasara a yayin da ta fita daga kurkukun Ofer na sojin Isra'ila da ke kusa da Ramallah a Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye./Hoto: Reuters
Bafalasdiniya Malak Salman wadda ta kwashe shekara takwas a gidan yarin Isra'ila ta sake haduwa da iyalinta a Beit Safafa da ke Gabashin Birnin Kudus bayan an sake ta./Hoto: AA
Marah Bakr (Hagu), wata Bafalasdiniya da ta kwashe shekara takwas a kurkukun Isra'ila, ta isa gida wurin iyayenta a Gabashin Birnin Kudus bayan an sake ta./Hoto:AA
Raghad Fan (Tsakiya), wata Bafalasdiniya da aka saka daga kurkukun Isra'ila, ta hadu da 'yan uwanta a Baytunia da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye./Hoto:AA