Sport
Dollar
40,7883
0.03 %Euro
47,7961
0.05 %Gram Gold
4.407,3600
0.17 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban UNRWA, Philippe Lazzarini, ya ce an kashe dubban yara a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza, sannan an mayar da yawansu marayu ko an firgita su.
Fiye da yara 100 sun mutu saboda rashin abinci da tsananin yunwa a Gaza yayin da Isra'ila ta tsananta ƙawanyar da take yi yankin, in ji shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa (UNRWA).
“Aƙalla yara 100 sun mutu saboda rashin abinci da yunwa,” in ji Babban Kwamishinan UNRWA, Philippe Lazzarini, a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
Ya bayyana cewa mutuwar da ta faru saboda yunwa ta sa yawan yaran da aka kashe ko aka raunata ya haura 40,000 ta hanyar hare-haren sama da harbe-harben Isra'ila tun watan Oktoba 2023.
Lazzarini ya ce aƙalla yara 17,000 a Gaza ko dai “ba sa tare da iyaye ko an raba su da iyalansu,” kuma yara miliyan daya suna cikin tsananin damuwa kuma sun bar makaranta.
“Yara dai yara ne,” in ji shi. “Babu wanda ya kamata ya yi shiru idan yara suna mutuwa, ko kuma ana hana su makoma mai kyau a cikin zalunci, duk inda wadannan yara suke, ciki har da Gaza.”
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce a ranar Laraba mutane takwas, ciki har da yara uku, sun mutu cikin awanni 24 da suka gabata saboda yunwa da rashin abinci.
Wannan ya kawo jimillar wadanda suka mutu saboda yunwa zuwa 235, ciki har da yara 106, yayin da matsalar jin kai a yankin ke kara tsananta.
Comments
No comments Yet
Comment