Dollar

40,6876

0.18 %

Euro

47,4070

-0.18 %

Gram Gold

4.447,6100

0.29 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Firaminista Ousmane Sonko na Senegal ya yaba wa Turkiyya kan cigaba da tallafa wa Afirka, inda ya bayyana Turkiyya a matsayin ƙasa mai nuna 'yar'uwantaka da kere muradun Senegal.

Erdogan ya yaba wa Senegal kan goyon bayan Falasɗinu, ya soki manufofin Yamma kan Afirka

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yaba wa matsayin Senegal kan sukar tsayuwar daka da take yi game da zaluncin Isra'ila, yana mai cewa goyon bayansu ga al'ummar Falasɗinawa wanda ke zaman misali ne ga ƙasashe da dama.

“Za mu yi ta fafutuka har sai an kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza, kuma waɗanda suke jefa yara marasa laifi cikin yunwa da mutuwa sai sun fuskanci hukunci,” in ji Erdogan, yayin wani taron manema labarai tare da Firaministan Senegal, Ousmane Sonko, a ranar Alhamis.

Erdogan ya bayyana cewa dangantakar Turkiyya da Senegal, wata ƙasa ce mai muhimmanci kuma 'yar uwa ga nahiyar Afirka, kuma tana ci gaba da bunƙasa.

Ya ce, a ganawa da suka yi ranar Alhamis, sun tattauna kan damar haɗin-kai tare da Sonko, musamman a ɓangaren zuba jari da cinikayya, da kuma tsaro, da masana'antar tsaro, yaƙi da ta'addanci, makamashi, haƙar ma'adinai, sufuri, noma, da kamun kifi.

Shugaban Turkiyya ya bayyana cewa Ankara na da burin ƙara yawan cinikayya da Senegal zuwa dala biliyan 1 a farko, sannan daga baya zuwa dala biliyan 3.

Sonko ya yaba da goyon bayan da Turkiyya ke bayarwa, yana mai bayyana ta a matsayin ƙasa 'yar uwa wadda koyaushe take tare da Senegal.

Yayin da yake jaddada ƙarfin masana'antar tsaron Turkiyya, ya ce dangantakar ƙasashen biyu na ƙara ƙarfi a hankali.

Sonko ya kuma nuna godiya ga Erdogan saboda kasancewarsa ɗaya daga cikin shugabannin da suka nuna adawa da kisan kiyashin Isra'ila a Gaza.

“Muna farin ciki da yadda 'yan uwarmu na Afirka ke kara sha'awar kayayyakin tsaron Turkiyya. Muna fatan kara karfafa hadin kanmu a wannan fanni a nan gaba,” in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#