Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya faɗa wa Trump cewa yana bin diddigin yarjejeniyar tsagaita wuta da haɗin kai da aka ƙulla ƙarƙashin jogarancin Amurka da gwamnatin Syria.

Erdogan da Trump sun tattauna kan Syria da Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da Shugaban Amurka Donald Trump inda suka taɓo dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu da yanayin da ake ciki a Syria da ƙoƙarin Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza, da kuma ci-gaban yankuna da na duniya.

Turkiyya za ta ci gaba da ɗaukar matakai don inganta haɗin gwiwa da Amurka da kuma ciyar da dangantakarsu gaba a dukkan fannin muradun ƙasashen biyu, in ji Erdogan a ranar Talata.

Ya kuma jaddada cewa Turkiyya tana mayar da hankali sosai kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da haɗin kai a Syria maƙwabciyarta, kuma Ankara tana sa ido sosai kan tsarin da aka kafa tare da haɗin gwiwar hukumomin Amurka da Syria.

Ya kuma bayyana fatansa ga Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza kan ya cim ma sakamako mai kyau.

Erdogan ya ce ya yi imanin cewa kawo ƙarshen rikicin jinƙai a Gaza da sake gina yankin zai share fagen samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Trump ya sanar da kafa "Kwamitin Zaman Lafiya" a ranar 15 ga Janairu a matsayin wani ɓangare na shirinsa a faɗin Gaza, wanda a ƙarƙashinsa aka cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta. Daga baya ne kwamitin ya samu izini daga ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 2803 a watan Nuwamban 2025.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#