Dollar

43,3725

0.25 %

Euro

51,3279

0.73 %

Gram Gold

6.945,5100

1.57 %

Quarter Gold

11.455,2500

2.32 %

Silver

142,9700

6.92 %

Yayin ganawar a ziyara ta farko da Tuggar zai kawo Turkiyya, ana sa rai Fidan zai bayyana gagarumar rawar da Nijeriya take takawa wajen wanzar da zaman lafiya a Yammacin Afirka.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da takwaransa na Nijeriya za su gana kan cinikayya da tsaro

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai gana da takwaransa na Nijeriya Yusuf Tuggar, wanda zai kai ziyara Ankara ranar Litinin, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya na Turkiyya.

Yayin ganawar a ziyara ta farko da Tuggar zai kai Turkiyya, ana sa rai Fidan zai bayyana gagarumar rawar da Nijeriya take takawa wajen wanzar da zaman lafiya a Yammacin Afirka.

Kazalika ana sa rai ministan harkokin wajen na Turkiyya zai fayyace matakan da ƙasashen biyu za su ɗauka wajen kyautata alaƙar cinkayya da zuba jari, ciki har da batutuwan da suka shafi buƙatun kamfanonin Turkiyya.

Haka kuma Fidan zai bayyana buƙatar kyautata haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu a fannin soji da tsaro, da kuma muhimmancin haɗa gwiwa wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci.

Tattaunawa kan Gaza da Somalia

Ministan zai jaddada muhimmancin haɗa kai tsakanin ƙasashen biyu a cikin ƙungiyoyin ƙasashen duniya irin su Majalisar Ɗinkin Duniya, Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai (OIC), da Ƙasashe Takwas Masu Cigaban Tattalin Arziki (D-8).

Fidan zai nuna buƙatar kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya tsakanin Turkiyya da Nijeriya — waɗanda duka mambobi ne na Kungiyar OIC-Arab League Gaza Contact Group — domin tabbatar da tsagaita ya ɗore a Gaza, tare da kyautata yanayin jinƙai a yankin da kuma samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.

Ministan harkokin wajen na Turkiyya zai kuma bijiro da buƙatar haɗa kai tsakanin Ankara da Abuja wajen ganin an mutunta ‘yancin kan Somalia kamar yadda dokokin ƙasashen duniya suka amince.

An ƙulla alaƙar diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Nijeriya ranar 9 ga watan Nuwamba na 1960.

Bunƙasa cinikayya

Cinikayyar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta kai ta $688.4m a watanni 11 na shekarar 2025. Idan aka haɗa da batun makamashi, Nijeriya ce babbar ƙawar kasuwancin Turkiyya a yankin hamadaer Sahara a 2025.

Kamfanonin Turkiyya fiye da 50 ne suke hulɗar kasuwanci a Nijeriya, inda adadin cinikayyarsu ya kai $400m.

A shekarun baya bayan nan, an samu ƙaruwar ‘yan kwangilar Turkiyya a Nijeriya, inda suka yi aiki da ya kai na kusan $3bn.

A bisa tsarin Ankara na goyon bayan yaƙin da Abuja ke yi da ta’addanci, ƙasashen biyu suna ci gaba da kyautata haɗin kai a fannin soji da tsaro.

Daga shekarar 1992 zuwa 2023, ɗalibai 199 ‘yan Nijeriya suka kammala karatu a Turkiyya ta hanyar samun gurbin karatu daga Turkiyya. A halin yanzu, ɗalibai 149 ‘yan Nijeriya suna ci gaba da karatu a Turkiyya a tsarin bayar da gurbin karatu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#