Sport
Dollar
43,2784
0.04 %Euro
50,7593
0.66 %Gram Gold
6.620,2500
1.91 %Quarter Gold
10.936,4100
1.61 %Silver
131,1600
-0.06 %An gano makarantar islamiyyar ne a kusa da kabarin Melik Mehmed Gazi, daga ɓangaren kudu na Masallacin Kebir na yankin Kayseri na Turkiyya.
An tono da wata makarantar islamiyya da aka yi amannar ta kai kusan shekara 900 a birnin Layseri da tsakiyar yankin Anatolia, bayan da aka gano ɓaraguzan gininta a lokacin da ake wani aikin sabunta birnin, kamar yadda jami’an yankin suka ce.
An gano makarantar islamiyyar ne a kusa da kabarin Melik Mehmed Gazi, daga ɓangaren kudu na Masallacin Kebir na yankin Kayseri na Turkiyya, yayin da ake gudanar da ayyukan Shirin Sabunta Birni na Surici Camikebir.
Memduh Buyukkilic, magajin garin Kayseri, ya shaida wa Anadolu cewa birnin ya kasance mazaunin al'ummomi daban-daban kuma yana da wuri na musamman a tarihin Musulunci.
“Cami Kebir wani yanki ne da muke gudanar da aiki cikin kulawa da ma'ana,” in ji shi. “Yayin da muke tone yankin, mun gamu da abin mamaki. A gefen kabarin Melik Mehmed Gazi ne muka gano alamu da bangarorin wata makarantar islamiyya da aka gina cikin tsarin wani hadadden ginin addini (külliye).”
Melik Mehmed Gazi, wani shugaba daga Masarautar Danishmend, ana ɗaukar shi a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa Kayseri kuma muhimmin mutum a farkon tarihin Turkiyya-Musulunci a Anatoliya. Masallacin da ya gina har yanzu yana daga cikin manyan alamun tarihi na birnin.
Buyukkilic ya ce hukumar birnin za ta gudanar da ayyukan tonon ƙasa da na gyara tare da haɗin gwiwar Ma'aikatar Al'adu da Yawon Buɗe Ido, tare da la'akari da binciken masana da takardun tarihi da suka riga suka wanzu.
“Manufarmu ita ce farfaɗo da wannan makarantar islamiyya mu kawo abin tarihi mai daraja ga Kayseri, ga birninmu da ƙasarmu,” in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment