Dollar

43,1388

0.21 %

Euro

50,2459

-0.08 %

Gram Gold

6.246,2500

0.83 %

Quarter Gold

10.381,6000

0.77 %

Silver

110,7700

4.07 %

Majiyoyin tsaron Turkiyya sun shaida wa TRT World cewa Turkiyya tana bibiyar rikicin da ake yi a Syria don kare fararen hula da hana kwararar 'yan gudun hijira saboda yaƙin da ake yi a Aleppo tsakanin sojojin Syria da ƙungiyar ta'addanci ta YPG.

Turkiyya na sanya ido sosai kan rikici a Syria a wani bangare mai muhimmanci kan tsaron kasarta

Tyrkiyya ta ce tana sa idanu sosai kan halin da ake ciki a Siriya, inda aka ba da fifiko ga hadin kan siyasa na ƙasar, da kiyaye iyaka da tsarin gwamnatin ƙasa, kamar yadda bayanan da majiyoyin tsaro na Turkiyya suka shaida wa TRT World.

Hukumar Leƙen Asiri ta Kasa (MIT) tana mai da hankali kan rage tasirin rikice-rikicen yankunan kan iyaka a Turkiyya, tana bibiyar yiwuwar kwararar masu ƙaura daga cikin Siriya, da kuma taimakawa wajen tabbatar da tsaron fararen hula a yankin, in ji majiyoyin.

“Ana nazarin sabbin arangama a Aleppo, musamman a unguwannin Sheikh Maqsoud, Ashrafiyeh da Beni Zaid, inda ake da al’ummar Ƙurdawa da yawa, tsakanin rundunar soja ta Siriya da 'yan YPG,” in ji majiyoyin.

YPG ita ce reshen ƙungiyar ta’addanci ta PKK a Siriya.

Majiyoyin tsaro sun ce rikici ya barke ne bayan YPG ta kasa girmama yarjejeniyar 10 ga watan Maris da gwamnatin Siriya.

Ayyukan ƙungiyar, waɗanda ake ganin suna rushe ƙoƙarin sulhu, sun haifar da tsoro na ƙarin tabarbarewar zaman lafiya a yankin.

’Yan ta’addan YPG sun kashe akalla fararen hula takwas kuma sun tilasta wa dubban mutane yin hijira a cikin sabon tashin hankalin a Aleppo.

Gwamnatin Siriya ta daɗe tana bin hanyar magance rikicin ba tare da tashin hankali ba, kamar yadda majiyoyin tsaron suka jaddada, inda ta yi tayi masu yawa ga YPG tare da ci gaba da buɗe hanyoyin tattaunawa.

“Sai dai, YPG ta yi watsi da waɗannan tayin, sannan ta ɗauki matsayi mai tsauri, tana neman ƙarin lokaci,” in ji majiyoyin.

Kafa iko a yankunan da ake fafatawa

Rundunar soja ta Siriya ta karɓe iko da unguwannin Ashrafiyeh da Beni Zaid bayan fafatawa, in ji majiyoyin, yayin da ayyukan soji ke ci gaba a Sheikh Maqsoud.

Sojojin Siriya sun ayyana dakatar da kai hare-hare a yankunan da ake rikicin a Aleppo, suna bai wa YPG damar janyewa zuwa gabashin Kogin Furat don hana sake barkewar tarzoma.

Amurka da Turkiyya sun yaba da sanarwar tsagaita wutan da Damaskus ta yi, inda suka bayyana ta a matsayin hanyar hana ƙarin zubar da jini da kuma kwararar ‘yan gudun hijira masu yawa.

Ankara ta yi watsi da duk wani yunkuri na ƙungiyar ta’addancin YPG na amfani da fararen hula a matsayin garkuwa a cikin yakin da take yi da rundunar soja ta Siriya.

Turkiyya na ci gaba da neman warware tashin hankalin a Siriya cikin lumana, bisa ga ikon Siriya na ƙasa da martaba iyakokinta, in ji majiyoyin.

Dukkan hukumomi suna faɗake

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yana bibiyar ci gaban lamuran sosai, yayin da MIT ke ci gaba da tuntuɓar hukumomin Amurka da na Siriya tana isar da saƙonni, a cewar majiyoyin.

Ana kuma sa ido kan abubuwan da suke faruwa sosai tare da Ma’aikatar Harkokin Waje da Ma’aikatar Tsaron Kasa, yayin da ma’aikatan MIT a yankin ke aiki ba dare ba rana, cikin kwanaki 7 a mako, in ji majiyoyin.

Turkiyya ta jaddadawa a koyaushe cewa, ba za a iya raba zaman lafiya da tsaron Siriya da nata ba, tana kira ga duka ɓangarorinsu yi haƙuri su koma tattaunawa.

Majiyoyin tsaro sun jaddada cewa Kurdawan Siriya 'yan ƙasar ne, kuma kare haoƙƙoƙinsu na daga cikin abubuwan da Turkiyya ke fifitawa.

A cewar majiyoyin, babban burin Ankara shi ne samun zaman lafiya mai ɗorewa da kwanciyar hankali a Siriya tare da kiyaye dukkan iyakarta, kuma tana sa ran YPG za ta ɗauki wata hanya da za ta taimaka ga haɗin kan Siriya a siyasance, da zaman lafiya na al'umma, da haɗin kan al’umma a zamantakewa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#