Sport
Dollar
41,4171
0.21 %Euro
48,7056
-0.32 %Gram Gold
4.902,8900
1.34 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%‘Yan ta’addan sun kai hari garuruwa biyu a Jihar Borno waɗanda ke a kusa da iyakar Kamaru, lamarin da ya tilasta wa kimanin fararen hula 5,000 tserewa zuwa ƙasar ta Kamaru.
‘Yan ta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya sun kai hari a sansanin soja da daddare, lamarin da ya tilasta wa kimanin fararen hula 5,000 tserewa zuwa Kamaru, in ji majiyoyin tsaro da shaidu a ranar Juma’a.
A bana an sake fuskantar ƙaruwar tashin hankalin daga ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram da kuma reshenta na ISWAP suka haddasa, inda duka biyun suka shafe lokaci mai tsawo suna tayar da ƙayar baya a ƙasar da ke yammacin Afirka.
Harin daren da aka kai garuruwan Banki da Freetown, wanda ke kusa da iyakar Kamaru, ya faru ƙasa da mako biyu bayan wani hari da aka kai wa mutanen da aka sake tsugunarwa sakamakon rikici a Darul Jamal, inda aka kashe kusan mutane 90.
Shaidu sun ce ƙungiyar Boko Haram ce ta kai harin, inda mayaƙanta suka afka Banki kusan ƙarfe goma sha biyu na dare, kuma wani farar hula ya rasa ransa a musayar wuta tsakanin sojoji da maharan.
“Sojoji sun yi bajinta sosai”
“Ko’ina mutane suna ihu suna gudu,” in ji wata mazauniyar Banki mai suna Amina Bakari, wadda ta tsere ta haye iyaka zuwa Kamaru.
Comments
No comments Yet
Comment