Sport
Dollar
41,3799
0.21 %Euro
48,7235
-0.14 %Gram Gold
4.870,5000
0.67 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta ce matsalar ta soma ne a lokacin da tawagar hukumar ta tabbatar da bin dokar ta isa harabar kamfanonin ranar Laraba, kuma ma’aikata suka kai musu farmaki.
Gwamnati jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Nijeriya ta ta rufe kamfanonin ‘yan China guda biyar da ke Ogere a kan hanyar Legas zuwa Ibadan bayan ma’ikatan kamfanonin sun tsangwami jami’an gwamnatin masu tabbatar da bin doka.
Kamfanonin da lamarin ya shafa sun haɗa da DL Plastics Limited da Dyschenghan Plastics da SH Agricultural Limited da Beautiful Fibre Limited da kuma Jincaicai Nigeria Limited.
Rahotanni daga Nijeriya sun ce kamfanonin sun yi watsi da saƙonnin gayyata da hukumar kwashe shara ta gwamnatin jihar Ogun ta tura musu game da zargin aikata ba daidai ba kan muhalli.
Wata sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis ta ce matsalar ta soma ne a lokacin da tawagar hukumar ta tabbatar da bin dokar ta isa harabar kamfanonin a ranar Laraba, kuma ma’aikata suka kai musu farmaƙi.
Sanarwar ta ce farmakin ya janyo “raunuka a jikin jami’an ɗabbaka dokar da kuma jami’an gwamnatin jihar yayin da suka aitwatar da aikin hukuma.”
Da yake tabbatar da matakin ranar Alhamis, babban mai ba da shawara ga gwamnan jihar kan muhalli kuma babban daraktan hukumar OGWAMA, Abayomi Hunye, ya ce kamfanonin suna daɗaɗɗen tarihin bijrewa.
“Tun watanni shida suka gabata muke kan wannan maganar. Mun tura musu wasiƙu kuma mun gayyace su su zo su kare kansu, amma sun ƙi amsa gayyatar.
“Baya ga waɗannan wasiƙun, jami’anmu sun kai musu ziyara a wasu lokuta, amma sun ƙi su ba su damar shiga,” a cewar Hunye.
Ya ce gwamnatin ba ta da wani zaɓi face ta ɗauki mataki.
“Bayan dukkan waɗannan matakan suka ci tura, mun manna sanarwar niyyar rufe harabarsu, musamman muhimman ƙofofin shiga.
“Duk da haka sun ƙi ba da haɗin kai, saboda haka ranar Alhamis ɗin da ta gabata, jami’anmu sun rufe su ta hanyar garƙame ƙofofinsu. Abin da ya ba mu mamaki shi ne zun cire hatimin gwamnati tare da kacan da aka yi amfani da shi wajen garƙame su”
Comments
No comments Yet
Comment