''Cikin watanni ukun da suka gabata, CBN ya yi nasarar rage bashin kudaden da ake binsa, wanda ya kai kusan dalar Amurka biliyan biyu,” a cewar mukaddashin mai magana da yawun Bankin, Hakama Sadi Ali a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.
Babban bankin Nijeriya CBN ya biya kusan dala biliyan biyu a matsayin bashin kudin kasashen waje na FX a cikin watannin uku da suka gabata a wani mataki na rage yawan kudin dala da ake bin kasar.
Mai magana da yawun bankin ta bayyana cewa, sai dai har yanzu karancin kudaden na ci gaba da haifar da mummunan tasiri ga kudin Naira na kasar.
Akwai akalla dala biliyan 7 na kudaden kasuwannin kasashen waje FX da suka makale a kasar da tafi kowacce kasa karfin tattalin arziki, lamarin da ya sanya fargaba a zukatan masu zuba jari, sai dai babban bankin kasar CBN ya yi alkawarin biyan kudaden don bai wa kasuwar canjin kudi ta duniya kwarin gwiwa.
''Cikin watanni ukun da suka gabata, CBN ya yi nasarar rage bashin kudaden da ake binsa, wanda ya kai kusan dalar Amurka biliyan biyu,” a cewar mukaddashin mai magana da yawun Bankin, Hakama Sadi Ali a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.
“Wannan yana jaddada irin kokarin da Bankin ke yi wajen magance matsalolin da suka kunno kai tare da inganta kasuwar canji.''
Karancin kudaden kasashen waje a Nijeriya ya fuskanci koma baya tare da tasiri a fannin hako mai da ke zama mafi girman abu da kasar ke fitarwa zuwa kasashen waje da kusan kashin 90 cikin 100 na kudin dalar Amurka da ke shiga kasar.
A cewar Sadi Ali, a baya-bayan nan CBN ya biya dala miliyan 61.64 ga kamfanonin jiragen sama na kasashen waje, wadanda suka sayar da tikiti a farashin kudin kasar na Naira amma ba su samu damar fitar da kudadensu daga kasar ba.
Zuwa karshen watan Nuwamba kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suna bin sama da dala miliyan 700.
“Wadannan kudaden na nuni da irin kokarin da CBN ke yi na daidaita tare da rage duk wasu basussuka da ake bin kasar da nufin rage matsin lamba a kan farashin canji a kasar,” in ji Sadi Ali.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi alkawarin bunkasa kudaden kasashen waje da ke shigowa kasar ta hanyar jawo sabbin masu zuba jari, da habaka hako mai da kuma gyara kasuwar canji a Nijeriya.