Wani dalili da ya ƙona ran masoya Barcelona shi ne yadda Ancelotti bai ambaci batun raunin Raphinha ko ƙoshin lafiyarsa ba, yayin jawabinsa na bayan wasa.

Barcelona ta fusata da Ancelotti kan raunin da Raphinha ya samu a wasan Brazil da Australia

Rahotanni daga Sifaniya na cewa ƙungiyar Barcelona da masoyanta sun fusata da jin labarin raunin da aka ce tauraron ɗanwasansu, Raphinha ya samu yayin da yake buga wa ƙasarsa Brazil wasa.

Fushin ‘yan Barca ya tattara kan kocin tawagar Selecao, Carlo Ancelotti, wanda ke jagorantar Brazil a wasannin sada-zumunta. Ancelotti dai tsohon kocin babbar abokiya hamayyar Barca ne, Real Madrid.

Barcelona na fargaba kan lafiyar Raphinha wanda kafin tafiyarsa wasannin ƙasa-da-ƙasa yake kan ganiyarsa ta cin ƙwallaye, kuma yake zaman kyaftin ɗin Barca.

Zargin da suke wa koci Ancelotti shi ne ba ya barin Raphinha ya huta, abin da ake tunanin ya janyo ɗanwasan ya samu rauni a wasansu da Australia lokacin hutun rabin lokaci.

Endrick ne ya maye gurbinsa, amma kafin nan sai da ya ci ƙwallo ta fenareti a wasan da Brazil ta yi nasara da ci 4-2. Ƙwallon da ya ci ta kawo ƙarshen kwanaki 500 da ɗanwasan ya yi rabonsa da ciyo wa Brazil ƙwallo.

Girman fargaba

Barca na fargabar Raphinha zai je hutun jinya na tsawon lokaci, wanda zai iya shafar tagomashin ƙungiyar wadda a yanzu take jan ragamar teburin La Liga.

Wani dalili da ya ƙona ran masoya Barcelona shi ne yadda Ancelotti bai ambaci batun raunin Raphinha ko ƙoshin lafiyarsa ba yayin jawabinsa na bayan wasa ga manema labarai.

Maimakon maganar raunin, kocin ya yi ta yabon wani tauraron Brazil da shi ma ya ci ƙwallo guda a wasan, Vinicius Jr, wanda kuma ɗanwasan Real Madrid ne.

Sai dai hukumar ƙwallo ta Brazil, (CBF) ta hanzarta fitar da sanarwa da ke tabbatar da gwajin likita da aka yi wa Raphinha, wanda ya nuna akwai "ƙaramin" kumburin oedema a tsokarsa.

Wani ƙarin dalilin damuwa kan Raphinha shi ne kasancewar Raphinha yana da tarihin raunin a cinyarsa, wanda ko a kakar bara sai da ya yi jinyar kwanaki 150 sakamakon jerin raunuka huɗu a cinyarsa ta dama.

#